Saudiya Da Iran Za Su Kai Wa Juna Ziyarar Diflomasiya

Iran ta ce nan gaba kadan jami’an diflomasiyar kasashen biyu za su ziyarci Saudiya domin fahimtar juna a wani yunkuri na dinke sabani da barakar da ke tsakaninsu bayan sun yanke hulda a bara.

Saudiya Da Iran Za Su Kai Wa Juna Ziyarar Diflomasiya

Ministan harkokin wajen Iran Mohammed Javad Zarif ya bayyana haka lokacin da ya ke jawabi ga daliban kasar, inda ya ce za a yi ziyarar ne bayan kammala aikin Hajjin bana. Zarif ya ce tuni aka ba jami’an da za su gudanar da ziyarar iznin shiga kasashen, abin da suke jira kawai shi ne mataki […]

An zargi Saudiyya da ‘yada ta’addanci’ a Birtaniya

An zargi Saudiyya da ‘yada ta’addanci’ a Birtaniya

Wani sabon rahoto ya bayyana cewa Saudiyya ce ke rura wutar yaduwar tsattsauran ra’ayin addini a Birtaniya. Kungiyar kwararru ta Henry Jackson Society ta ce, “Akwai alaka mai karfi” tsakanin kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayin addini ta yadda suke samun kudi, da masu da’awa mai tsauri da kuma kungiyoyin jihadi da ke yada ta’addanci. Kungiyar ta […]

‘kwalara ta yi sanadin mutuwar mutum 1,500 a Yemen’

‘kwalara ta yi sanadin mutuwar mutum 1,500 a Yemen’

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ba da sanarwar cewa mutum 1,500 ne a yanzu suka mutu sakamakon ɓarkewar cutar amai da gudawa a Yemen. Ƙasar dai a yanzu tana fuskantar ɓullar cutar amai da gudawa ko kwalara mafi muni a duniya. Cutar wadda ke yaɗuwa ta hanyar ruwa na bazuwa cikin hanzari a faɗin Yemen […]

Kotu ta amince Trump ya hana Musulmi shiga Amurka

Kotu ta amince Trump ya hana Musulmi shiga Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi maraba da hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke wanda ya ba shi damar hana Musulmi daga wasu kasashe shiga kasar, yana mai cewa hakan “wata nasara ce ga tsaron kasa”. Kotun kolin ta kuma amince da wani bangare na bukatar fadar White House ta hana ‘yan gudun hijira […]