Najeriya ta cafke ‘yan China da ke hakar ma’adinai ta haramtaciyar hanya

Hukumomin Najeriya sun kama wasu ‘yan kasar China 8 da ake zargi da hakar ma’adinai a Jihar Plateau ba tare da izini ba.

Najeriya ta cafke ‘yan China da ke hakar ma’adinai ta haramtaciyar hanya

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Ali Monguno ya bada umurnin kama mutanen bayan ya ziyarci inda suke aiki a garin Bashar da ke karamar hukumar Wase tare da ministan ma’adinai Kayode Fayemi. Minista Fayemi ya kuma bayyana cewa Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osibanjo ya bada umurnin rufe wurin hakar ma’adinan da […]