Gwamnatin Najeriya Zata Taimakawa Jahar Nija Ta Wadata Afirka Da Abinci

Mukaddashin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ne ya bayyan haka a Minna fadar jahar Nija.

Gwamnatin Najeriya Zata Taimakawa Jahar Nija Ta Wadata Afirka Da Abinci

Gwamnatin tarayyar Najeriya zata hada karfi da gwamnatin jahar Nija dake arewacin Najeriya, wajen bunkasa harkokin noma, da zummar ciyar da kashi 50 cikin dari na al’umar nahiyar Afirka. Mukaddashin shugaban Najeriya Parfessa Yemi Osinbanjo, shine ya bayyana haka lokacinda yake bikin bude taron bunkasa harkokin kasuwanci na kwanaki biyu a Minna, babban birnin jahar. […]