Ana Zaman Dar-dar a Yankin Madagali Sanadiyar Sabon Harin Boko Haram

Tun daga yammacin jiya ne mayakan Boko Haram dauke da muggan makamai suka farma kauyen Bakin Dutse cikin karamar hukumar Madagali, a jihar Adamawa kuma kawo yanzu ba’a tantance adadin mutanen da wannan sabon harin ya rutsa dasu ba.

Ana Zaman Dar-dar a Yankin Madagali Sanadiyar Sabon Harin Boko Haram

Kamar yadda wasu da suka tsallake rijiya da baya suka bayyana, mayakan na Boko Haram dauke da muggan makamai, sun soma kai farmaki ne daga yankin Bakin Dutse dake kusa da garin Gulak hedikwatar karamar hukumar suna harbe-harbe ba kakkautawa inda aka dauki dogon lokaci ana dauki ba dadi a tsakaninsu da sojoji da kuma […]

Kungiyar Boko Haram Ta Sake Kai Hari a Yankin Madagali Dake Jihar Adamawa

Mayakan Boko Haram sun kai wani sabon hari a Kuda dake yankin Madagali, cikin jihar Adamawa a arewa maso gabashin kasar,inda suka kona gidaje da sace abinci kamar yadda suka saba yi a 'yan kwanakin nan.

Kungiyar Boko Haram Ta Sake Kai Hari a Yankin Madagali Dake Jihar Adamawa

Mayakan Boko Haram sun kai wani sabon hari a Kuda dake yankin Madagali, a jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya Yankin Madagali yana gaf da bakin dajin Sambisa inda ‘yan ta’addan Boko Haram suke samun mafaka. A wannan harin, kamar yadda suka saba yi a yankin, sun kone gidaje, kaddarori tare da sace abinci […]