Jam’iyyar APC ta mika sunayen ‘yan takara daga Zamfara

Jam’iyyar APC ta mika sunayen ‘yan takara daga Zamfara

Hukumar zabe wato INEC ta ce tana nan kan bakanta game da kin amincewa da sunayen ‘yan takarar jam’iyyar APC daga jihar Zamfara, duk kuwa da wani hukunci da kotu ta yanke a kan al’amarin. Hukumar ta ce a ta ta fahimtar umarnin kotun yana nuni ne da cewa kowa ya tsaya a kan matsayin […]

‘Yan Bindiga Sun Sace ‘Yan Sanda 3 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Sace ‘Yan Sanda 3 A Zamfara

Wasu mutanen da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sace ‘yan sanda uku dake aiki a wata caji ofis din ‘yan sanda a garin Keta na Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara. ‘Yan bindigar  da har yanzu ba a san ko suwanene ba dauke da bundugu sun isa kyauyen inda suka kaiwa Caji Ofis din […]

Gwamnatin Tarayyar Najeriya Za Ta Hada Jihohi Uku da Layin Dogo

Ministan sufuri Amaechi ya fada a Sokoto gwamnatin tarayya na shirin hada jihohin Zamfara, Kebbi da Sokoto da layin dogo irin na zamani

Gwamnatin Tarayyar Najeriya Za Ta Hada Jihohi Uku da Layin Dogo

Kokarin gwamnatin tarayyar Najeriya na hada jihohin Zamfara, Kebbi da Sokoto da layin dogo ba zai tabbata ba sai da amincewar Majalisar Dattawa a cewar ministan sufurin kasar. A cewarsa tuni gwamnati ta tura bukatar zuwa majalisar. Rotimi Amaechi wanda shi ne ministan sufuri a karkashin shugabanci Muhammad Buhari yace jihohin uku da ake son […]

Jami’ar Gusau Ta Bijirewa Matakin Hukumar JAMB

A bayan nan ne shugaban hukumar shirya jarabawar shiga jami'o'i da manyan makarantu a tarayyar Najeriya Farfesa Is-haq Oloyede ya sanar da kayyade maki 120 a matsayin wanda za a rika bai wa dalibai gurbin karatu a jami'o'in kasar dashi

Jami’ar Gusau Ta Bijirewa Matakin Hukumar JAMB

Wasu Jami’o’I a tarayyar Najeriya sun fara nuna halin ko’in kula kan matakan da hukumar shirya jarabawar shiga jami’oi da sauran manyan makarantu ta kasar, JAMB ta gindaya, kan rage makin samun gurbin karatu ga dalibai zuwa maki 120 ga mai neman jami’a da kuma 100 ga sauran manyan makarantu. Jami’ar tarayya ta Gusau a […]

Kallo Ya Koma Jihohi, A Yunkurin Samawa Kananan Hukumomi ‘Yanci.

Shugaban kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi komored Ibrahim khalil yace zasu addu'o'i na musamman kan wannan yaki.

Kallo Ya Koma Jihohi, A Yunkurin Samawa Kananan Hukumomi ‘Yanci.

    Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta Najeriya, tace yanzu zata maida hankali kan majalisun dokokin jihohin Najeriya 36, a kokarin ganin cewa jihohin sun amince da kudurin da majalisun tarayya suka amince da shi na baiwa kananan hukumomin ‘yancin cin gashin kansu. Shugaban kungiyar komored Ibrahim Khalil, yace ‘yan kungiyar mabiya dukkan addinai, wani […]

Talakawa sun hana sarki shiga fadarsa a Zamfara

Al'ummar garin Boko na jihar Zamfara a arewacin Nigeria, sun yi wata zanga-zanga don nuna rashin amincewa da yunkurin mayar da basaraken garin wanda suka kora daga garin; kan mulki.

Talakawa sun hana sarki shiga fadarsa a Zamfara

Mutanen dai na zargin Sarkin ƙayan Moriki, Abubakar Ahmad Rufa’i da ƙwace musu gonaki, da kuma hada kai da jami’an tsaro don cin zarafinsu, koda yake basaraken ya musanta zarge-zargen. Basaraken dai ya arce daga garin na Boko ne wanda ke a Karamar Hukumar Zurmi ta jihar Zamfara ne a watannin baya, saboda fusatar da […]