An rantsar da Emmerson Mnangagwa sabon shugaban Zimbabwe

An rantsar da Emmerson Mnangagwa a matsayin sabon shugaban kasr Zimbabwe, a wani biki da dumbin jama'a suka taru makil a filin wasa na Harare, babban birnin kasar.

An rantsar da Emmerson Mnangagwa sabon shugaban Zimbabwe

Hakan ya biyo bayan yin murabus da Shugaba Robert Mugabe ya yi ne, bayan shekara 37 da ya shafe yana mulkin ‘kama-karya.’ Korar da Mista Mugabe ya yi wa mataimakin nasa a farkon watan nan ce ta jawo jam’iyya mai mulki ta Zanu-PF da kuma sojoji suka tursasawa Mugabe yin murabus. Mr Mnangagwa, wanda a […]

An bai wa Mugabe wa’adin sauka daga mulki ko a tsige shi

Tsoffin kawayen shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, sun yi kakkausar suka ga matakin da ya dauka na yin biris da kiraye-kirayen da ake masa a kan ya yi murabus.

An bai wa Mugabe wa’adin sauka daga mulki ko a tsige shi

Shugaban kungiyar ‘yan mazan jiya, Chris Mutsvangwa, ya shaida wa BBC cewa, an riga an gama da Mr Mugabe a fagen siyasa domin babu wani tasiri da zai yi. Mai magana da yawun jam’iyyar kasar mai mulki ta Zanu-PF ya ce, yanzu Mr Mugabe ba shi da wani iko. Jam’iyyar wadda tuni ta cire shi […]

An yi tir da ba Robert Mugabe mukamin farin jakada

An yi tir da ba Robert Mugabe mukamin farin jakada

Kungiyoyin kare hakkin dan’adam da jam’iyyar adawa a Zimbabwe sun yi tir da shawarar Hukumar Lafiya a Duniya ta nada Shugaba Robert Mugabe matsayin farin jakada Kungiyar Human Rights Watch ta ce la’akari da tarihin Mugabe kan batun ‘yancin bil’adama, abin kunya ne ba shi irin wannan mukami. Jam’iyyar adawa a Zimbabwe ta ce matakin […]

Me ya sa shugabannin Afirka ke zuwa kasahen ketare jinya?

Shugabannin kasashen Najeriya da Angola da Zimbabwe da Benin, da Algeria na da abubuwan da suke kamanceceniya, wato rashin yarda da tsarin kiwon lafiyar kasashensu.

Me ya sa shugabannin Afirka ke zuwa kasahen ketare jinya?

Ta fuskar lokutan da suka shafe suna jinya a kasar waje, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari mai shekara 74, shi ne na farko a cikinsu, amma a shekarun da suka gabata dukkan wadannan shugabannin sun ketara wasu kasashen don duba lafiyarsu. A lokuta da dama suna tafiya su bar asibitoci ba isasshen kudin da za […]

Bankuna a Zimbabwe za su fara karbi dabbobi a jingina

Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe ya saka hannu kan wata sabuwar doka da za ta ba kananan masana'antu da 'yan kasuwa damar su bayar da dabbobi da wasu kayan amfani a gida a zaman jingina wajen samun bashi.

Bankuna a Zimbabwe za su fara karbi dabbobi a jingina

Hukumomin kasar dai sun ce an kafa dokar ne domin shawo matsalar rashin jari da kananan masana’antu ke fuskanta sakamakon halin da tattalin arzikin kasar ke ciki. Wannan dokar ta bai wa bankuna kasuwanci a Zimbabwe damar su karbi dabbobi kamar shanu, da awaki, da kuma tumaki a zaman jingina wajen bayar da rancen kudi. […]

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe ya yi hatsarin mota a Harare

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe ya yi hatsarin mota a Harare

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya yi hatsarin mota yayin da yake barin filin jirgin saman birnin Harare bayan ya dawo daga tafiya. Ko da yake, shugaban bai ji rauni ba, amma mai dakinsa Grace wadda suke tare a mota ta jikkata. Shugaban ya sauka a filin jirgin saman ne yayin da ya dawo jinya […]