Talakawa sun hana sarki shiga fadarsa a Zamfara

Al'ummar garin Boko na jihar Zamfara a arewacin Nigeria, sun yi wata zanga-zanga don nuna rashin amincewa da yunkurin mayar da basaraken garin wanda suka kora daga garin; kan mulki.

Mutanen dai na zargin Sarkin ƙayan Moriki, Abubakar Ahmad Rufa’i da ƙwace musu gonaki, da kuma hada kai da jami’an tsaro don cin zarafinsu, koda yake basaraken ya musanta zarge-zargen.

Basaraken dai ya arce daga garin na Boko ne wanda ke a Karamar Hukumar Zurmi ta jihar Zamfara ne a watannin baya, saboda fusatar da jama’arsa suka yi da yadda suka ce yake kwace musu filaye yana saida wa masu hali- abin ya kai suka lalata fadarsa.

Rahotanni sun nuna dambarwar ta faro ne bayan mutanen garin sun zargi basaraken da kwace wa kimanin mutum 70 gonaki shekaru biyu da suka wuce a karon farko.

Karo na biyu kuma a bana ya sake kwace wa mutum 65 ta hanyar aika shanu su cinye amfanin gona da damina, sannan daga baya sai ya nemi kowa ya fanshi gonarsa, wadanda suka gaza yin haka kuma sai a sayar da nasu ga wani mai hali.

A ranar Talata mahukuntan jihar suka yi kokarin mayar da shi garin, amma hakan ya gamu da turjiya daga mutanen garin.

”Haka kwatsam sai muka gan shi tare da kwamishinan ‘yansanda ya rako shi tare da ‘yansandan dauke da makamai, wai da karfin tsiya sai sun shigar da shi gidan sarauta. Mu kuma talakawa muka yi tunanin komai na iya faruwa, don haka muka yi zanga-zanga ta lumana.” In ji wani mazaunin garin.

Sai dai sarkin Kayan Moriki Abubakar Ahmadu Rufa’i ya musanta zargin inda ya ce Fulani makiyaya ne suka yi korafi kan mamaye musu mashaya kuma burtali a yankin, matsalar da sarkin ‘Burmin Moriki Alhaji Isma’ila Ari na II ya ba shi umarnin ya warware.

Karanta:  BOKO HARAM: Amurka Ta Sake Alkawarin Taimaka Ma Najeriya

Ya ce ya je garin na Boko ne bisa gayyatar kwamishinan ‘yansanda, Alhaji Shaba Alkali, wanda ya je rangadi don ganin inda za a bude caji ofis.

Sai dai, kwamishinan ‘yansandan ya ce sun je garin ne don raka basaraken kwaso sauran dukiyarsa, bayan ya shafe kusan wata shida rabonsa da garin sakamakon lalata masa fada.

“Basaraken yana da kadarorinsa da yake so ya kwashe don haka ya ce a taimaka masa. Shi yasa muka je, amma da ganinsa sai matasan garin suka dauko makamai. Sai da muka kai zuciya nesa.”

Asalin Labari:

BBC Hausa

946total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.