Taraba: Rikici Ya Barke a Jam’iyyar APC

Wani sabon rikici ya sake barkewa a jam’iyar APC reshen jihar Taraba yayin da tsohon mukaddashin gwamnan jihar Garba Umar UTC, ke sauya sheka zuwa jam’iyar.

Tuni da wasu kusoshin jam’iyar APC suka kafa wata sabuwar tafiya da suka kira kansu kungiyar yan integrity.

Su dai kusoshin jam’iyyar da suka hada tsoffin Sanatoci da tsohon shugaban jam’iyar a jihar da yan Majalisu da kuma masu ruwa da tsaki a siyasar jihar, sun ce sun kafa wannan sabuwar tafiyar ne domin ceto jam’iyar daga abin da suka kira halin ha’ula i da suke zargin wasu sun jefa jam’iyar a ciki.

Da yake jawabi a wajen taron da suka gudanar shugaban wannan tafiya wanda tsohon mataimakin gwamna ne a jihar Alhaji Uba Maigari Ahmadu, ya ce ba wata sabuwar APC suka kafa ba, a’a sabuwar tafiya ce kawai domin ceto jam’iyar daga rugujewa tare da nuna bara’arsu ga wasu shugabanin jam’iyar na jihar.

To sai dai kuma a martanin da ya maida shugaban riko na jam’iyar APC a Taraba, Alhaji Sani Chul, dake tare da bangaren Ministan harkokin mata da walwalar jama’a Aisha Jummai Alhassan, ya musanta zargin cewa basa tafiya da kowa.

Shi dai wannan sabon rikicin na zuwa ne yayin da tsohon mukaddashin gwamnan jihar Taraban Alhaji Garba Umar UTC, ke komawa jam’iyar wanda kuma yanzu lokaci ne ke iya tabbatar da yadda za’a kaya a wannan sabuwar dambarwa.

Asalin Labari:

VOA Hausa

825total visits,1visits today


Karanta:  An Yanka Ta Tashi a Kan Maganar Wa'adi Ga 'Yan Kabilar Igbo

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.