Taya Murnar Dawowar Buhari da Dr. Abdullahi Umar Ganduje Yayi a Kano

Mabiyan a karkashin lemar Patriotic Nigerians wanda mataimaki na musamman akan kafafen yada labarai na shugaban kasa Muhammadu Buhari wato Sha’aban Ibrahim Sharada yake jagoranta tare da addu’a Allah ya karawa shugaban kasar lafiya da kuma murnar dawowar shi gida lafiya

A yau alhamis 24 ga watan Agusta gwamnar jahar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya karbi dimbin mabiya da masoya wadanda suke nuna murnar da farin ciki da dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari, mabiyan sun hadu a filin wasa na Sani Abacha inda akayi sallah da addu’o’I daga nan aka dungumo zuwa sha tale talen gidan gwamnati Golden Jubilee.

Mabiyan a karkashin lemar Patriotic Nigerians wanda  mataimaki na musamman akan kafafen yada labarai na shugaban kasa Muhammadu Buhari wato Sha’aban Ibrahim Sharada yake jagoranta tare da addu’a Allah ya karawa shugaban kasar lafiya da kuma murnar dawowar shi gida lafiya.

Gwanna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya mika godiya ga al’umar da suka hallaci wurin, yakara da cewa wannan shine abun da Kasa ta ke bukata wato zaman lafiya da hadinkai ga al’uma, kuma hakan zai kara karfafa gwiwar shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ya cigaba da ayyukansa na alkhari.

Asalin Labari:

Muryar Arewa

741total visits,1visits today


Karanta:  'Maganar Fatar Baki Ba Za Ta Magance Matsalar Tsaro Ba'

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.