Taylor Swift tayi nasara a shari’ar ta da David Mueller

Mawakiya Taylor Swift ta samu wata gagarumai nasara a wata shari’ah da ta shiga tare da wani tsohon ma’aikacin gidan radio David Mueller bayan wata kotu ta zartar da hukunci akan karar da ya shigar kan cewar Swift ce ta sanya aka kore shi daga aikin sa sakamakon zargin kusantar ta da yayi.

Swift ta zargi Muller da yunkurin taba ta a yayin wani taro da aka gudanar a watan Yuni na shekarar 2003. Alkalin ya zartar da hukuncin bisa tarar dala 1 da Muller zai biya Swift sakamakon batanci.

Alkalan da suka hada da mata shida da kuma maza biyu, sun wanke mahaifiyar mawakaiyar mai suna Andrea Swift a bisa zargin yin katsalandan.

Bayan zartar da hukuncin, Taylor Swift ta rungume mahaifiyar ta ta.

A jawabinta, Swift tayi godiya ga alkalan tare da kungiyar lawyoyin ta.

627total visits,1visits today


Karanta:  Justin Bieber ya samu kutsawa cikin jerin masu kudin London

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.