Tillerson ya kai ziyarar tankwabe fada-a-jin Iran

Sakataren wajen Amurka Rex Tillerson ya isa birnin Riyadh don fara ziyarar kwana shida a Saudiyya da kuma makwabciyarta Qatar.

Tillerson zai sake matsa lamba don kawo karshen kaurace wa Qatar da Saudiyya tare da wasu kawayenta suka yi saboda zargin mara baya ga musulmi masu tsattsauran ra’ayi.

Sai dai ana sa rai ziyarar ta Tillerson za kuma ta mayar da kai wajen tankwabe karuwar fada-a-jin da Iran ke samu a Gabas ta Tsakiya.

Haka kuma, Tillerson zai kuma kaddamar da taron jami’an Saudiyya da Iraqi don kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu da nufin wargaza tasirin gwamnati a birnin Tehran.

Amurka dai na fatan cewa wannan dangantaka za ta kara karfi idan har kasashen larabawa ‘yan sunni suka amince da bayar da tallafi wajen sake gina biranen Mosul da Raqqa, wanda aka lalata a yayinda gwabzawar da ake da ‘yan kungiyar IS.

Gwamnatin shugaba Trump dai tana cikin matukar damuwa akan zaman doya da manjar da ake tsakanin kasashen da ke makwabtaka da juna a yankin na gabas ta tsakiya.

Mr Tillerson dai ya ce bashi da kwarin gwiwar da zai iya cewa zaman doya da manjar da kasashen ke ciki zai zo karshe nan bada jimawa ba, dole sai an dauki lokaci kafin komai ya daidaita tsakanin Qatar din da sauran kasashen da ke fama rikici.

Asalin Labari:

BBC Hausa

2422total visits,1visits today


Karanta:  FBI Ta Ce Nakiya Ce Ta Fashe Cikin Masallaci a jahar Minnesota

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.