Togo na Nazarin Takaita Wa’adin Shugaban Kasa

Yan adawa sun kaddamar da zanga-zanga a sassan Togo

Majalisar zartarwar Togo ta amince da shirin sanya wa’adin shugaban kasa a cikin kundin tsarin mulkin kasar sakamakon zanga zangar da ‘yan adawa suka kaddamar.

Daukar matakin zai bada damar gabatar da kudirin ga Majalisar dokoki domin yin doka akai.

Mutane sama da dubu dari ne suka gudanar da zanga-zanga a cikin birane 10 na kasar Togo, inda suka bukaci gwamnatin shugaba Faure Gnassingbe ta aiwatar da sauye-sauye ciki har da dawo da wa’adin shugabancin kasar sau biyu kawai.

Shugaba Faure Gnassingbe da ya hau karagar mulki a shekarar 2005 yanzu haka yana wa’adi na uku bayan ya gaji mahaifinsa da ya kwashe shekaru 38 a karagar mulki.

Asalin Labari:

RFI Hausa

387total visits,1visits today


Karanta:  Gobara ta tashi a sansanin 'yan gudun hijirar Syria

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.