Trump na fuskantar bore kan rikicin Charlottesville

Shugaban Amurka Donald Trump na fuskantar bore tun bayan furta wasu kalamai kan rikicin kabilancin daya faru a Charlottesville, al’amarin da yanzu haka ke ci gaba da sanyaya guiwar magoya bayansa, har ta kai ga murabus din wani babban jigo a tafiyar shugaban.

Lamarin dai ya buda sabon babi a tafiyar mulkin Shugaba Trump tun bayan fara aikinsa sama da kwanaki dari biyu.

Kalaman na Trump dai na zargin bangarorin 2 da alhakin tayar da tarzomar wadda ta girgiza dan karamin garin na Charlottesville da ke Jihar Virginia, tare da sanadin mutuwar wata mace guda cikin masu zanga-zangar adawa da kabilancin bayan da wata da wani mamba a kungiyar mai ra ‘ayin kabilanci ke tukawa ta yi awon gaba da ita

Shugaba Trump dai ya yi kasasabar da ta janyo murabus din mashawartansa uku, bayan da ya dora alhakin abinda ya farun kan bagarorin 2, masu kyamar kabilanci da kuma masu nuna kabilanci farar fata.

Wadannan kalamai da ke dauke da guba da zargi a lokaci guda da suka fita daga bakin shugaban na Amruka, sun samu yabo da jinjina daga tsohon shugaban kungiya mai ra’ayin kabilanci ta farar fata zalla Ku Klux Klan al’amarin da ya zumde da dama daga cikin zababbun wakilan al’umma a kasar.

Sai dai kuma sakamakon hango katafariyar Taguwar Ruwan dafa kansa da iska ya kwaso daga teku ne, ya tilasta wa shugaban a jiya Talata kiran wani taron yan jarida a fadar white house inda ya yi tir da duk wani nau’in rikicin kabilanci a kasar.

Shaidar da ke tabbatar da cewa kalaman na Trump sun yi muni sosai ne, ya hana jam’iyarsa ta Republican kasa fitowa fili ta kare (shi) tsohon mai arzikin ma’abucin gidajen alfarma a kasar ta Amruka

A wata hira da tashar talabijin ta ABC, shugaban jam’iyar ta Republican Ronna Romney McDaniel ya ce abinda ya faru a Charlottesville, babu shakka kungiyar Ku Klux Klan ce ke da laifi.

Karanta:  Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe ya yi hatsarin mota a Harare
Asalin Labari:

RFI Hausa

586total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.