Tsohon shugaban kasar Ghana ya gargadi ‘yan Najeriya kan kabilanci

Jerry John Rawlings

Tsohon shugaban kasar Ghana Mr Jerry John Rawlings, ya gargadi ‘yan Najeriya kan maganganu wadanda zasu ka iya kawo tashin hankula tare da rarrabuwar kai a kasar a tsakanin al’ummar kasar.

Da yake jawabin a jiya a wajen wani taro da kungiyar dalibai ta Jami’ar Ibadan reshen jihar Ekiti ya shirya wanda shine karo na goma sha biyu da aka gudanar.

Rawlings, wanda shine bako na musamman a wajen taron, ya shawarci ‘yan Najeriya dasu daje wajen samar wa da kansu shuwagabanni na gari a lokutan zabe domin samun jagororid masu kishin kasa.

Yayi karin bayani da cewa matsalolin rayuwa ka iya zuwa sakamakon rashin samun shugabanci na gari. Don haka yayi kira ga al’umma su hada su zama tsintsiya madaurin ki daya. Ya kara da cewa idan Najeriya ta yaki cin hanci da rashawa, zai zama riba ce gaba daya ga kasashen Afrika baki daya.

647total visits,2visits today


Karanta:  Ko Kunsan Kasar Da Ake Damawa Da Mata A Wasan Tamola?

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.