Turkiyya ta saki sautin kisan Kashoggi

Jamal Kashoggi

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya bayyana cewar ya kasar sa ta baiwa kasashen Amurka, Birtaniya, Jamus da Saudiya sautin kisan dan jaridar nan mai sharhi Jamal Khashoggi dan kasar Saudi Arabiya.

Shugaban na Turkiyya Erdogan ya sake nanata cewar Saudiya ta san wadanda suka kashe Jamal Khashoggi.

Jamal Khashoggi dai ya kasance fitaccen mai sukar gidan sarautar kasar Saudiya ne kafin kisan nasa a ofishin jakadancin kasar da ke birnin Istanbul ranar biyu ga watan Oktoba na 2018.

Da farko dai kasar ta Saudiya musanta kisan na sa, sai dai daga bisani ta amince da cewa an kashe shi a cikin ofishin nata, ko da yake ta jaddada cewa babu hannun ‘yan gidan sarautar kasar.

187total visits,3visits today


Karanta:  Masar ta sallama wa Saudiyya iko da tsibirai

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.