Wa’adin Neman a Tsige Mahaifin Nnamdi Kanu Daga Sarauta Ya Cika

Wa'adin da wata kungiyar matasa ta bai wa gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, na ya tsige mahaifin Nnamdi Kanu, Israel Okwu Kanu daga sarautarsa, ya cika, inda suka zarge shi da kin ja wa dansa kunne kan fafutukar da yake yi wacce suka ce ta kassara harkokin yau da kullum a yankin.

Nnamdi Kanu

Wa’adin da wata kungiyar matasa a garin Umuahia ta bai wa gwamnatin jihar Abia na ta tsige Israel Okwu Kanu, mahaifin shugaban fafutukar neman kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu daga mukamin sarautar garin Isiamah Afaraukwu ya cika.

A farkon makon nan kungiyar matasan ta ba da wa’adin ga gwamna Okezie Ikpeazu inda ta yi barazanar cewa za ta dauki doka a hanu muddin ba a biya mata bukatarta ba.

Kungiyar matasan ta zargi basaraken da kasa takawa dansa Nnamdi Kanu birki kan fafutukar da yake yi ta kafa Biafra, wacce suka ce ta janyo durkushewar kasuwanci da harkokin yau da kullum a garin Umuahia.

“Kafin a tsige sarki akwai tsarin da ake bi, ba za ka wayi gari kawai ka ce za ka tsige shi ba, ba lallai ba ne mu san abinda shi baban ya sha fadawa dansa.” In ji Amanzo Okpara, wani mazaunin Birnin Umuahia.

“Bai da ce a tsige mahaifin Kanu ba saboda abubuwan da ke faruwa a fadarsa, Nnamdi Kanu ba yaro ba ne, idan ya baro abinda za a kai shi gidan yari, shi za a daure ba uban ba.” A cewar John Uzoma.

Yanzu dai ya rage ne a ga abinda zai biyo bayan cikar wannan wa’adi wanda kungiyar matsan ta bayar.

Wata arangama da aka yi tsakanin ‘ya’yan kungiyar IPOB a makon da ya gabata a garin Umuahia ta kai ga kassara harkokin yau da kullum a garin.

Asalin Labari:

VOA Hausa

735total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.