Wadanne Batutuwa Buhari ya Taras a Nigeria?

Komawa gida da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi a ranar Asabar bayan kwashe sama da wata uku yana jinya a Landan za ta taso da batutuwa daban-daban.

Shugaban, wanda ya fice daga kasar ranar takwas ga watan Mayu domin yin jinyar cutar da ba a bayyana ba, ya mika mulki ga mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo.

Tun daga lokacin da ya bar kasar, mukaddashin shugaban kasar ya gudanar da ayyuka da dama da suka hada da rantsar da sabbin ministoci da bai wa manyan jami’an rundunar soji umarnin komawa Maiduguri don tunkarar Boko Haram, da sauransu.

 

Rashin tsaro

Daya daga cikin manyan matsalolin da Shugaba Buhari zai taras ita ce ta rashin tsaro a kusan kowane bangare na kasar.

Tun bayan tafiyar shugaban kasar Burtaniya kungiyar Boko Haram ta kara kaimi wurin kai hare-hare a arewa maso gabashin kasar musamman a jihar Borno.

Kungiyar ta kai hare-hare kunar bakin wake da dama, musamman a Jami’a Maiduguri da ma wasu yankuna na jihar Borno.

Sai dai abin da ya fi jan hankali shi ne harin da ta kai wa ma’aikata da ke hakar man fetur inda ta kashe da dama daga cikinsu sannan ya yi garkuwa da wasu.

Hakan ya tilasta wa mukaddashin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo tura manyan jami’an rundunar soji birnin Maiduguri domin dakile hare-haren ‘yan Boko Haram. Amma har yanzu ba a saki ma’aikatan da ke hakar man ba.

Haka kuma akwai matsalar sace mutane domin karbar kudin fansa musamman a hanyar Kaduna zuwa Abuja, da ta matsafan kungiyar badoo da ke Lagos da sauransu.

Rabawa ko sake fasalin Najeriya

Wata matsalar da ke jiran Shugaba Buhari ita ce ta ‘yan kungiyar IPOB masu rajin ganin yankin kudu maso gabashin kasar ya balle daga Najeriya.

Kungiyar, karkashin jagorancin Nnamdi Kanu, ta sha alwashin yin amfani da makamai domin cimma burinta.

Karanta:  An kama masu kitsa kai hare-hare biranen arewacin Nigeria

Kuma tun bayan tafiyar shugaban kasar Ingila kungiyar ke ci gaba da yin kalaman batanci domin dai ta tunzura ‘yan kasar.

Da alama kuma ta cimma burinta domin kuwa wata kungiya da ke ikirarin magana da yawun matasan arewacin kasar ta bai wa ‘yan kabilar Igbo wa’adin ranar daya ga watan Oktoba kan su bar yankin saboda, abin da ta kira, butulcin ‘yan kabilar ta Igbo.

Lamarin da ya dada rikita halin da kasar ke ciki inda wasu gwamnonin arewacin kasar suka janye kansu daga wannan umarni har ma gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Elrufai ya ba da umarnin a kama matasan.

Wannan batu dai ya sa masu son sake fasalin Nigeria sun matsa kaimi kan bukatar tasu, abin da ya sa jam’iyyar APC mai mulki ta nada kwamitin da zai jagoranci wannan batu daga bangarenta.

Yaki da cin hanci

Wannan batu na cikin manyan alkawuran da Shugaba Buhari ya sha alwashin magancewa tun lokacin da yake yakin neman zabe.

Tun da ya bar kasar hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta ci gaba da aikinta ko da yake tana ci gaba da fuskantar kalubale.

EFCC ta yi nasara wajen ganin kotu ta mallakawa gwamnatin kasar makudan kudade d kadarorin tsohuwar ministar mai Diezani Allison-Madueke da wasu tsofaffin jami’an gwamnatin da ake zargi da sace kudin kasar.

Sai dai har yanzu ba ta iya daure mutanen da ake zargi da satar ba don haka wasu ‘yan kasar ke ganin akwai aiki a gaban shugaban kasar.

 

Karanta:  'Rashin fita zaɓe na kassara shugabanci nagari'

Wani abu kuma shi ne yadda ake cacar baki tsakanin bangaren zartarwa da majalisar dattawa kan tabbatar da shugaban riko na EFCC Ibrahim Magu kan kujerarsa.

‘Yan kasar za su so ganin yunkurin da Shugaba Buhari zai yi wajen ganin majalisar, wacce ta saba laya kan Mr Magu, ta tabbatar da shi kan mukamin nasa.

Rahoton kwamiti kan Babachir Lawal

Hakazalika ‘yan Najeriya za su so ganin shugaban kasar ya karbi rahoto kwamitin da ya binciki Sakataren gwamnatin tarayya.

A watan Afrilu ne dai shugaban ya dakatar da Mr David Babachir Lawal kan zargin cuwa-cuwa da kudin da aka ware domin bai wa ‘yan gudun hijirar da Boko Haram ta raba da gidajensu.

Sai dai ya musanta zargin.

Kwamitin, wanda ke karkashin mataimakin shugaban kasar, ya kammala bincikensa amma bai miki rahotonsa ba saboda fitar Shugaba Buhari zuwa jinya.

Ministoci

Tun ma kafin Shugaba Buhari ya fice daga kasar wasu ke ganin akwai bukatar ya yi tankade da rairaya a majalisar ministocinsa saboda rashin alkiblar wasu daga cikinsu.

Masu sharhi dai na ganin da dama daga cikin ministocin da masu ba shi shawara ba su da burin ci gaban Najeriya a zukatansu shi ya sa ma bangarori da dama ke fuskantar matsaloli.

Yanzu dai za a zuba ido a gani ko shugaban kasar zai iya yi wa majalisar ministocin nasa garambawul domin a samu sauye-sauye na gari kan lamura da dama.

Siyasa

Masu sharhi kan harkokin siyasar Najeriya na ganin cewa rashin lafiyar shugaban kasar ta sa masu kwadayin mulkar kasar sun soma wasa wukarsu da zummar ganin ba a bar su a baya ba.

Karanta:  Kotu ta daure basaraken da ya kitsa sace kansa gidan yari

Wasu na ganin Shugaba Buhari ba zai sake yin takara ba idan aka yi la’akari da yanayin jikinsa da kuma tsufa.

Sai dai watakila komawarsa kasar za ta bai wa ‘yan siyasa damar sanin matsayinsa wurin yin takara a 2019, alabishi hakan zai sa su san inda za su dosa.

Tuni dai ake hasashen cewa wasu manyan ‘yan siyasa na shirin sauya sheka daga jam’iyyar mai mulki idan ba za a tsayar da su takara a zaben 2019 ba.

Da alama komawar shugaban kasar gida za ta kuma yayyafa ruwa a zukatan masu gangamin ganin ya koma kasar ko kuwa ya sauka daga mulki saboda rashin lafiyarsa.

Yajin Aikin Malaman Jami’o’i

Har ila yau, akwai batun malaman jami’o’i wadanda suka fara yajin aikin sai abin da hali ya yi a ranar Lahadi.

Kungiyar malaman jami’ar kasar (ASUU) ta ce ta shiga yajin aikin saboda rashin aiwatar da yarjejniyar da ta cimma da gwamnatin a shekarar 2009.

Cikin batutuwan da kungiyar ke korafi a kai sun hada da rashin zuba isassun kudade a jami’o’i da rashin biyan malamai cikakken albashi da rashin biyansu ragowar kashi 60 cikin 100 na kudaden alawus-alwasu dinsu, wanda kungiyar ta ce duka an cimma yarjejeniya a kansu.

Asalin Labari:

BBC Hausa

963total visits,4visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.