Wani Darakta ya Kashe Kansa a Jihar Kogi

Wani Darakta mai shekaru 54 da haihuwa mai aiki a hukumar Koyarwa ta jihar Kogi mai suna Edward Soje ya kashe kansa ta hanyar rataye kan nasa a wata bishiya a garin Lakoja babban birnin jihar.

Kamfanin jaridar Daily Trust ranar Lahdi ya fahimci cewa an sami gawar ma’aikacin gwamnatin na reto a jikin wata bishiya dake bayan kasuwar sojoji dake Chari Maigumeri a garin Lakoja.

An gano cewa marigayin na fama da matsalolin da suka shafi kudi kafin faruwar lamarin kamar yadda wasu daga cikin iyalan marigayin suka bayyana

An dai ce lamarin ya faru ne kwanaki 10 bayan da matar daraktan mai shekaru 17 wadda bata taba haihuwa ba ta haifi jarirai uku rigis a wani asibitin kudi dake Abuja

An kuma ce daraktan ya barwa matartasa wadda ke aiki a daya daga cikin ma’aikatun gwamnatin tarayya wasikar kashe kan nasa.

Lokacin da aka tuntubi mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, Williams Aya, yace an sami gawar mutumin da misalin karfe 5:55 na yamma.

Aya yace DPO wanda ke iko da caji ofis din ‘yan sanda da ke yankin ‘D’ ya sami bayanan faruwar lamarin daga ofishin tsaro na soji dake barikin.

29151total visits,1visits today


Karanta:  Magajin Garin Sokoto Danbaba Ya Ajiye Rawaninsa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.