Wani Darakta Ya Kashe Kansa A Legas

Mr Oludare Buraimoh Mai Matsayin Mukamin Darakta ne a Ma’ikatar Matasa ta Jihar Legas ya kashe kansa ta hanyar rataya a cikin dakinsa

Buraimoh wanda ke zaune a rukunin gidajen Unity dake Gbonagun a Abeokuta ya kashe kansa ne da misalin karfe 4:00 na yamma ranar Litinin bayan da ya ziyarci dansa Dotun da bashi da lafiya.

Da yake bada jawabi Dotun cewa yayi lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:00 na yamma bayan da mahaifin nasa ya bashi maganin zazzabin maleriya dake damunsa.

“Dukkaninmu muna gida, yazo ya bani magana ya tafi ya barni tunani na a lokacin shi ne ya tafi dakinsa ne yaje ya huta. Lokacin da ban ji muryarsa ba, sai nayi kiransa, amma bai amsa ba.

“Nan take na tafi dakin nasa sai na sameshi da wata murtukekiyar waya sakar garin Aso Oke daure a wuyansa da kuma wata kujera wadda yayi amfani da ita wajen kashe kan nasa. Nan take na sanar da makota, su kuma suka ce min na sanar da ‘yan sanda, hakan kuwa nayi,” a cewar Dotun din.

Maidakin mamacin cewa tayi har yanzu bataje ta sheda abinda maigidan nata ya aikata ba

Shi kuwa DSP  Rasheed Olaleye na caji ofis din Obantoko inda lamarin ya faru tabbatar da faruwar lamarin yayi. NAN

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

727total visits,1visits today


Karanta:  Rikici ya barke tsakanin al'ummar Hausawa a Lagos

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.