Wani Mutum Ya Cakawa Kansa Wuka Sannan Yayi Tsalle Ya Fada Rijiya

Wani mutum mai shekaru 40 a duniya, mai suna Balarabe Adamu ya cakawa kansa wuka sannan yayi tsalle ya fada rijiya  ranar Talata a unguwar Rijiyar Zaki dake Karamar Hukumar Ungogo.

Alhaji Mustapha Rilwan, Darakta a Ma’aikatar Kashe Gobara ta Jihar Kano shi ne ya fadawa Kamfanin Dillancin Labarai na NAN cewa sun same ceto mutumin daga cikin rijiyar amma daga baya mutumin ya mutu a asibitin Kwararru na Murtala Muhammad dake Kano

Yace makotan mutumin ne suka sanar da hukumar kashe Gobarar cewa Balarabe yayi tsalle ya fada rijiya bayan da ya cikawa kansa wuka.

“Daga jin haka, nan da  nan muka tura jami’anmu a mota inda lamarin ya faru da misalin karfe 5 na yamma, a cewar Daraktan Hukumar Kashe Gobarar.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

431total visits,1visits today


Karanta:  Me Marubutan Nigeria Keyi a Lebanon?

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.