Wanne Mataki Buhari Zai Dauka Kan Babachir?

Hankulan wasu 'yan Najeriya sun karkata zuwa irin matakin da shugaban Najeriya zai dauka kan sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya da shugaban hukumar leken asirin Najeriya da aka dakatar kan zarginsu da aikata ba-dai-dai-ba.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya dai ya karbi sakamakon binciken da aka gudanar kan zargin almundahana da ake yi wa manyan jami’an gwamnatinnasa biyu ne a ranar Laraba.

A watan Afrilu ne dai shugaban ya umarci wani kwamiti karkashin jagorancin mataimakinsa ya binciki sakataren gwamnatin kasar da kuma shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta NIA, bayan dakatar dasu bisa zarge-zarge daban-daban na almundahana.

Sai dai a bangare guda fadar shugaban ta sanar da dage zaman majalisar ministoci da ya kamata ya shugabanta a yau a karon farko cikin watanni da dama.

Tun a ranar 8 ga watan Mayu ne aka shirya shugaban kasar zai karbi rahoton amma sai rashin lafiyarsa ta hana hakan, inda ya koma Landan don ganin likita ranar 7 ga watan Mayu.

Asalin Labari:

BBC Hausa

685total visits,1visits today


Karanta:  Yadda Jonathan ya kassara Najeriya-Fadar Shugaban Kasa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.