Wasu Iyaye Sun Mayar Da Martani Game Da Zargin Mikawa ‘yan Boko Haram ‘ya’yansu

Wasu iyaye a birnin Maiduguri jihar Borno, arewa maso gabashin Nigeria, sun maida martani ga zargin da rundunar soja tayi cewa, wasu iyaye da kansu suke baiwa yan Boko Haram 'ya'yansu.

Wasu magidanta a jihar Borno, arewa maso gabashin Nigeria sun mayar da martani ga zargin da hafsan sojojin Nigeria ya yi cewa, wasu iyaye da kansu, suke baiwa ‘yan kungiyar Boko Haram ‘ya’yansu domin aiwatar da hare-haren kunar bakin wake.

Kusan dukkan wadanda suka bayyana ra’ayinsu ga wakilin Sashen Hausa Haruna Dauda biyu ba su amince da wannan zargin ba.

Misali daya daga cikin mutane ya ce, sai da idan “mutum mahaukaci” ne zai dauki dansa ko ‘yarsa ya bai wa ‘yan kungiyar Boko Haram domin a yi amfani da su wajen kai hare-haren kunar bakin wake.

Asalin Labari:

VOA Hausa

501total visits,1visits today


Karanta:  "Dole gwamnatin Najeriya ta kare 'yan gudun hijira"

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.