Wasu Masallata 2 Da Dan Sanda Daya Sun Rasa Ransu Sakamakon Kutsawar Wata Babbar Motar Itace Cikin Taron Idi A Ijebu Igbo.

An tabbatar da rasuwar wasu masallata biyu ’yan awannin kadan da suka shude, sakamakon kutsawar wata babbar motar itace cikin mahalartar sallar idin da aka gabatar yau din nan  a garin Ijebu Igbo, na Jihar Osun

Haka kuma wani Dan sanda ya rasa ransa dalilin kubucewar harsashi jim kadan bayan barkewar hatsaniya kan lamarin, abun da ya jefa daukacin al’umar yankin cikin dimuwa da jimami.

Wani cikin shaidun gani da ido yace birki ne ya daukewa babbar motar kafin tayi awon gaba da wasu dandazon masalata, ta kashe mutanen biyu, goma kuma suka samu muggan raunuka.

Wani wanda yazo halartar sallar idin, Alh. Ademola Balogun KLASS fadawa majiyarmu ta wayar tarho cewa shi da iyalansa sun tsallake rijiya da baya amma motarsa kirar Toyota Tundra mai lamba  APP 995 DD ta fita daga hayyacinta.

“ Banga dalilin barin wadannan motocin aiki yau ba. Ni da iyalin mun tsallake rijiya da baya. Maganan da nake daku mutum uku sun mutu. Abun babu kyau da safiyar nan. Abun tambayar anan shi ne mai zai sa abar wadannan motocin aiki yau? Manene dalilin barinsu? Balogun ke tambaya.

Bayanai sunyi nuni da cewa dan sandan ya rasa ransa sakamakon harbin iska da ‘yan sandan suka ringayi domin tarwatsa masu zanga-zanga kan babbar motar da masu motar.

Wani magidanci a Atikori yayi nuni da cewa tuni direban motar Ope Suleiman dan garin Oke Agbo  ya cika wandonsa da iska,. Shugaban cigaban yankin na Ijebu Igbo, Goke Adekunbi ya roki jama’a dasu kwantar da hankalinsu inda ya tabbatar  da cewa zasu dauki dukkanin matakin da ya dace kan lamarin.

Karanta:  Badaƙalar Biliyan 2.1: Maina Ya Ƙalubalanci EFCC …Ya Ce Yana Bin Gwamnati Bashin Biliyan 159

Sannan yayi addu’a ga mamatan.

 

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

2146total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.