Wasu Mata Biyu ‘Yan Kunar Bakin Wake Sun Rasa Ransu A Maiduguri

‘Yan sanda a Borno ranar Asabar sunce wasu mata biyu ‘yan kunar bakin wake sun rasa ransu lokacin da suka tada ababan fashewar dake daure a jikinsu a wajen birnin Maiduguri.

A sanarwar da Kakakin ‘Yan Sandan Jihar DSP Isuku Victor ya sakawa hannu a Maiduguri yace mutum 8 sunji rauni sakamakon faruwar lamarin.

Victor yace lamarin ya faru ne ranar Jumma’a da misalin karfe 17:38 na yamma lokacin da matan ‘yan kunar bakin waken suka tada ababan fashewar dake daure a jikinsu kusa da wata motar tasi kan titin Maiduguri zuwa Mafa.

“Wasu mata biyu ‘yan kunar bakin wake sun tada ababan fashewar dake jikinsu kusa da wata motar tasi kan titin Maiduguri zuwa Mafa kusada shingen binciken ababan hawa na Hukumar Kula da Safara da Shan Miyagun Kwayoyi a wajen birnin Maiduguri.

“’Yan kunan bakin waken ne kawai suka mutu, sai kuma mutum takwas wanda ya hada da Jami’in Hukumar Kula da Safara da Shan Miyagun Kwayoyi suka ji rauni wanda yanzu haka ake kulawa dasu.

“Tasin mai numba XA 479 DRZ na dauke da buhunhunan gwawayi ne sai kuma fasinjoji 2 mata a ciki, haka kuma wani babur mai kafa uku shima harin ya shafe shi,” a cewarsa.

Victor ya kara da cewa ‘yan sanda na musamman sun ziyarci wajen da lamarin ya faru kuma tuni mutane suka cigaba da gudanar da al’amuransu yanda aka saba a wajen da lamarin ya faru.

Mr Abdullahi Danbatta, Shugaban Sashin Ceto na Kungiyar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar yace ana kulawa da wadanda sukaji raunin a Asibitin Kwararru na Maiduguri.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

450total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.