Wata Mata Ta Kashe Kanta Saboda Mijinta Zai Yi Mata Kishiya

Wata matar aure mai shekaru 22 da haihuwa, mai suna Hajara Bala ta kashe kanta yayinda ta fahimci cewa mijinta na shirin kara aure.

An rawaito cewa marigayiyar ‘yar kyauyen YanMallam dake Karamar Hukumar Miga ta kwankwadi maganin bera ne don bazata iya rayuwa taga mijinta da wata matar ba.

Majiyar kamfanin jaridar Daily trust ta fahimci cewa an ruga da marigayiyar zuwa asibitin Jahun  dake Karamar Hukumar Jahun bayan data sha maganin beran ranar Litinin da misalin katfe 7 na yamma daga gidan mijin nata amma da misalin karfe 9 na yamman ta rigamu gidan gaskiya.

Haka kuma an ce shekaru kamar bakwai da suka gabata irin wannan lamarin ya faru a wannan garin inda wata makusanciyar marigayiyar ta kwankwadi irin wannan maganin beran itama saboda mijinta na shirin kara aure, sai dai ita bata mutu ba.

Mai Magana da Yawun ‘Yan Sandan Jihar SP Abdul Jinjiri ya tabbatar da faruwar lamarin.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

651total visits,4visits today


Karanta:  Hukumar SSS Ta Damke Wasu Kwamandojin Kungiyar Boko Haram

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.