Wata ta kama Mijinta yana yi wa ‘yar shekara 10 fyade akan gadonta

‘Yan sanda a karamar hukumar Ringim da ke jihar Jigawa sun kama wani mahauci da ake zargi da yin lalata da wata yarinya ‘yar shekara 10 a dakin matarsa bayan matar ta tafi unguwa.

Mahaucin mai suna Magaji Muhammed, mai kimanin shekara 53 dubunsa ta cika ne bayan da matarsa ta yi masa ihu lokacin da ta kama shi yana yin fyade ga yarinyar ( wacce aka sakaye sunanta ) a kan gadonta.

Rahoton Hausa Daily ya nuna cewa, hakan ne ya sa mahaifin yarinyar Hussaini Udu ya sanar da ‘yan sandan karamar hukumar Ringim halin da ‘yarsa take ciki inda ya ce, mahaucin ya yaudari yarinyar ce ta amince ta bi shi zuwa gidansa inda ya sata a dakin matarsa saboda yana da tabbacin matar ba za ta dawo da wuri ba ya fara yi mata fyade.

Mahaucin ya ce, yana fara yi wa yarinyar fyade kenan sai matarsa ta dawo ta kama shi da yarinyar akan gadonta.

Da ya ke amsa tambayoyin ‘yan sanda Magaji Mainama ya ce, ya aikata laifin yin lalata da karamar yarinya a dakin matarsa inda ya kara da cewa ya dauki lamarin a matsayin tsautsayi.

Asalin Labari:

Mujallarmu

2897total visits,1visits today


Karanta:  Gwamnatin Buhari 'Ta Kai Karar Mutum 6,646 Kotu a Shekara Daya'

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.