Watanni hudu da suka gabata ne kungiyar ‘yan Shiya reshen jihar Kano ta gurfanar da gwamnatin Kano da kwamishanan ‘yan sandan jihar da kwamishanan shari’a na jihar gaban babbar kotun tarayya dake Kano

Kungiyar na zargin wadanda ta gurfanar da cin zarafin da kuma kisan gilla da ta ce sun yiwa ‘ya’yanta yayinda suke tattaki zuwa garin Zaria a watan Maris din bara.

A cewar kungiyar matakin da jami’an tsaro suka dauka akan ‘ya’yanta tamkar tauye hakkinsu ne na gudanar da addinin da suke so. Kungiyar ta ce ‘ya’yanta na da ‘yancin kai komo da kuma kafa ko shiga kungiyar da suke muradi kamar yadda kundun tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Barrister Saleh Muhammad Bakaro lauyan ‘yan Shiya ya ce kafin gwamnatin tarayya ta yiwa kungiyar rajista sai da ta tabbatar babu abun da ya sabawa kasa ko addinin Muslunci a kundun tsarinsu ko kuma ya tauye hakkin wani.

Akan wadanda ya ce ‘yan sanda sun kashe lauyan yana neman kotun ta basu diyyar Naira miliyan dari biyar.

Sai dai a zaman kotun jiya Litinin lauyar gwamnati Barrister Halima Yahuza Ahmed ta ce kotun bata da hurumin sauraren karar saboda haka ta tsame hannunta. Ta ce wata kotun ya kamata ta saurari karar.

Za’a ci gaba da karar ranar 30 ga wannan wata na Nuwamba idan Allah ya kaimu.

Asalin Labari:

VOA Hausa

682total visits,3visits today


Karanta:  Matan Kungiyar Shi’a Sun Bukaci Gwamnatin Tarayya Data Saki El-Zakzaky

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.