Yadda aka kashe masu garkuwa da mutane a Taraba

Jama’ar gari sun hallaka wadansu mutum biyar da ake zargi da satar mutane suna karbar kudin fansa a garuruwan Tella da Gazabu da ke kananan hukumomin Gassol da Bali a Jihar Taraba, inda a garin Tella aka kashe mutum hudu da ake zargi da sace mutanen.

Jama’ar gari sun hallaka wadansu mutum biyar da ake zargi da satar mutane suna karbar kudin fansa a garuruwan Tella da Gazabu da ke kananan hukumomin Gassol da Bali a Jihar Taraba, inda a garin Tella aka kashe mutum hudu da ake zargi da sace mutanen. Sai dai wani da ake tuhuma mai suna Salihu Kingo da ya sha da kyar ya kai kansa ga hedkwatar rundunar ’yan sandar jihar da ke Jalingo.

Wakilinmu ya gano cewa a daren Lahadin makon jiya ne wadanda ake tuhumar suka shiga garin Tella amma masu sa ido kan duk wanda ya shiga garin da dare, suka sanar da jama’a, inda jama’a da ’yan banga suka sa ido kuma suka gano suna kokarin sace wani dan kasuwa ne.

Wani da aka kama mutanen a kan idonsa da ya nemi a sakaya sunansa ya ce kusan wayewar gari ne aka kama wadanda ake tuhumar amma daya daga cikinsu mai suna Salihu Kingo wanda dan asalin garin Tella ne ya sulale tare da taimakon mahaifinsa.

Ya ce labarin kama wadanda ake tuhumar ya bazu a cikin gari da sauran kauyuka inda dubban mutane suka hadu wadansu mutane suka nemi a kashe wadanda ake tuhumar, yayin da wadansu suka nemi a mika su ga hukuma. Kuma ana cikin haka ne ’yan sanda suka iso suka nemi a mika musu mutanen hudu amma mutane suka ki.

Majiyar ta ce wadanda aka kashen sun ce suna da hannu a sace mutane a yankin, kuma an same su da wayar matar wani dan kasuwa da aka sace kwanan nan a yankin. Ta ce ana cikin gardamar yadda za a yi da wadanda ake tuhumar ne, sai wadansu daga cikin mutanen suka fara dukansu aka kashe su aka kone gawarwakinsu aka jefa a kogin garin.

Karanta:  Buhari ya cika kwanaki 100 na jinya a London

Majiyar ta ce an samu bindigogi da wasu makamai a hannun mutanen, kuma sun shaida wa wadanda suka kama su cewa iyayen gidansu na cikin daji wadansu kuma na cikin garin Jalingo. Sun shaida musu cewa Naira dubu 200 kacal aka ba su daga cikin Naira miliyan biyu da suka karba daga wani dan kasuwa da suka sace a makon jiya, kuma sun biya wanda suka karbi hayar bindigogi a hannunsa inda iyayen gidansu suka rike sauran.

Majiyar ta ce a bara an rusa wani gida da aka samu masu satar mutanen sun boye wani da suka sace har ma aka kama mai gidan aka mika wa ’yan sanda amma daga baya aka sake shi.

Majiyar ta ce mutum biyu daga cikinsu matasa ne ’yan asalin yankin, biyu kuma daga garin Jalingo suke.

A garin Gazabu da ke yankin Bali, an kashe mutumin da ake zargin shi ne shugaban masu sace mutane a kananan hukumomin Bali da Gashaka. Wanda aka kashen dan asalin Jihar Yobe ya dade a garin na Gazabu har yana gida da mata a garin, kuma an yi zargin yana da gidaje masu yawa da motocin haya a Yobe amma a gidan da yake zaune a garin na Gazabu ko zana babu. Majiyarmu ta ce an kama shi ne bayan wani mai satar mutane da ’yan sanda suka kama ya fallasa shi. Kuma wani ganau ya ce mutane sun kwace shi ne daga hannun ’yan sanda suka kashe shi.

Daga bara zuwa bana an sace sama da mutum 64 a kananan hukumomin Gassol da Bali, inda bayanai suka ce an biya sama da Naira miliyan 100 kudin fansa kafin sako su.

Karanta:  Sojin Nigeria sun yi wa 'yan Boko Haram 'ruwan wuta' a Sambisa

Kakakin ’Yan sandan Jihar Taraba DSP Dabid Misal ya tabbatar da kashe mutum biyar da ake zargi da satar mutanen a garuruwan Tella da Bali, inda ya ce ’yan sanda sun fara gudanar da bincike kan lamarin kuma za su ba da cikakken bayani kan lamarin nan ba da jimawa ba.

 

Asalin Labari:

Aminiya

1188total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.