Yadda ‘Yan Boko Haram Suka Juyar Da Kanmu – Wadanda Suka Tsira

Kwamandan’ wanda aka gano sunansa Auwal Isma’il ne ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai

Kwamandan Boko Haram Auwal Isma’il, daya tsira ya kawo kansa ga Hukuma

Wani dan kungiyar Boko Haram da ake kira da kwamanda a tsakanin ’ya’yan kungiyar, ya yi ikirarin cewa shi ne ya jagoranci sace ’yan matan Chibok daga makaranta a shekarar 2014.

‘Kwamandan’ wanda aka gano sunansa Auwal Isma’il ne ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da kafar labarai ta PRNigeria.

Fiye da ’yan mata 200 ne Boko Haram ta sace daga makarantar ta Chibok da ke Jihar Borno a watan Afrilun 2014, kuma kimanin 100 daga cikinsu har yanzu suna hannun kungiyar bayan da aka sako akasarinsu sakamakon tattaunawa da Gwamnatin Tarayya.

Isma’il wanda ya mika kansa ga sojojin Najeriya, ya shaida wa kafar labaran cewa ya kuma jagoranci manyan hare-haren da kungiyar ta kai, inda ya yi nadamar aika-aikarsa.

Kafar labarai ta PRNigeria ta ce, a daidai lokacin da ake fuskantar bukukuwan Babbar Sallar a karshen makon nan, wani babban kwamandan Boko Haram wanda ya taka gagarumar rawa a sace ’yan matan Chibok da kashe matasa a Madagali ya mika kansa, kuma ya yi ikirarin sanya hannunsa a zubar da jinin mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba tare da lalata dimbin dukiya a sassan Arewa maso Gabas na kasar nan.

A tattaunawarsa da PRNigeria a wajen wani tsaro na soja, tubabben dan Boko Haram din da ya mika wuya a Arewa maso Gabas, tsohon jigon ’yan ta’addan ya ce, ya yi nadamar tu’annatin da aka tilasta shi ya tafka ga bani Adam.

Kwamanda Auwal Isma’ila wanda yanzu haka yake ba sojoji hadin kai ta wajen ba su bayanai masu muhimmanci kan wurare da maboyar sauran manyan kwamandojin Boko Haram din, ya yi nadamar ta’asarsa wadda ya ce, ta saba wa nassoshin addini Musulunci da dama.

Isma’ila, ya bukaci sauran manyan kwamandojin kungiyar su mika wuya ga sojoji. “Ni da Abu Hafsat, wani kwamandan Boko Haram ne muka jagorancin mayakan kungiyar wajen sace ’yan matan Chibok.  Kuma mun jagoranci kai harin mamaya a garuruwan Gwoza da Bama da Barikin ’Yan sandan Kwantar da Tarzoma na Limankara da Bita da Bosso da Madagali da Chibok da Pulka da Firgi da kuma Mubi,” inji shi.

Ya kara da cewa: “A garin Madagali wanda shi ne mahaifata, ni da Adam bitiri da Abu Adam da Habu Kudama, wadansu manyan kwamandojin Boko Haram ne muka jagoranci harin shekarar 2014 inda muka kashe wadansu dalibai a makarantar Sakandaren Santaral da ke Sabon Garin Madagali. A daya daga cikin hare-haren, na sace (wadda ta zamo) matata Maryam, wacce ta haifa min ’ya’ya biyu a dajin Sambisa. Abin takaici ne da aka wanke min kwakwalwa aka sa na kauce hanya ba wai kawai a kan sace mutanena har ma na rika kashe su siddan. Ina cike da nadamar aika-aikana.”

Karanta:  An sake kai hari Jami'ar Maiduguri

Ya ce: “A lokacin yakin Konduga inda ni da sauran kwamandojin Boko Haram muka jagorancin harin ne na rasa kafata ta dama, kuma na yi kusan konewa. Duk da haka ban daina yakin ba. Sheikh Shekau ya bayar da umarnin a ba ni babur mai kafa uku, wadda na ci gaba da amfani da ita wajen kai hare-hare kafin na mika wuya.”

Ya bayar da dalilai da dama da suka sanya ya mika wuya ga sojojin Najeriya bayan da ya fahimci hudubobin yaudara da muguwar akida na shugabannin kungiyar da kuma miyagun ayyukan da ake tafka a wasu sansanonin Boko Haram.

Ya ce: “Na mika wuya ne ga sojoji bisa radin kaina, saboda na gaji da kisan rashin imani da yaki rashin kan gado. Na fahimci cewa mutanenmu sun koma ga yin sace-sace da duk wani mugun abu da ya saba wa koyarwar addinin Musulunci. Ana yi wa mata fyade, wasu lokuta a fili. Yara suna mutuwa saboda rashin abinci da cututtuka saboda yanayin rayuwa ya dada kunci. Kuma saboda babu abinci a sansanin, kullum mutane suna mutuwa saboda yunwa. Kuma zan ci gaba da bayar da hadin kai ga hukumomin tsaro wajen bayar da bayanai masu amfani kan yadda muke gudanar da ayyukanmu tare da fallasa maboyar kwamandojinmu.”

Idan za a tuna fiye da kwamandoji da mambobin Boko Haram 100 ne suka mika wuya ga sojoji a baya-bayan nan, bayan da suka fahimci cewa barnar da suke yi tana cutar da kasar nan da kuma kasashen makwabta da suka hada da Kamaru da Nijar da Chadi.

 

‘bangarorin Boko Haram suna son tattaunawa da gwamnati’

Karanta:  Neman 'yan Boko Haram ne ya kai mu ofishin MDD - Sojin Nigeria

Akwai alamun da suke nuna cewa bangarori biyu na kungiyar ’yan ta’adda ta Boko Haram suna son tattaunawa da Gwamnatin Tarayya.

Wani tsohon kwamandan kungiyar, Abdulkadir Abubakar wanda aka fi sani da Abu Muhammad ne ya bayyana haka.

Abu Muhammad, wanda shi ne babban jami’in leken asiri na kungiyar Boko Haram, kuma daya daga cikin manyan kwamandojinta, sojoji ne suka kama shi a watan Yuni a garin Buni Yadi, hedkwatar karamar Hukumar Gujba da ke Jihar Yobe.

Abubakar ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a inda ake tsare da shi a Maiduguri cewa bangaren Albarnawi da Mamman Nur suna son hada kai da gwamnati domin a murkushe jagoran Boko Haram, Abubakar Shekau.

Ya ce, Shekau, wanda babban hafsan sojin kasar nan ya bayar da umarnin a kamo shi a raye ko a mace, yana kawo cikas ga zaman lafiya tun lokacin da aka fara kai hare-haren ta’addancin a shekarar 2009.

An ruwaito shi yana cewa: “Shekau ba ya son ya mika wuya saboda tsabagen girman kansa. Kuma abin takaicin gwamnati da sojoji sun fi bayar da fiffiko wajen tattaunawa da Shekau wanda mashayin jini ne. Albarnawi ya nuna sha’awarsa ta tattaunawa da gwamnati don kawo karshen ayyukan ta’addanci tare da kawo karshen rikicin. Albarnawi ya tattauna wannan batu da mambobinsa. Kuma ina ba gwamnati tabbacin cewa zai bayar da hadin kai a samu zaman lafiya. bangarorin biyu suna shirye domin hada kai da gwamnatin Najeriya a murkushe Shekau.”

Sai dai babu tabbas kan da’war Abubakar game da niyyar bangarorin biyu na sulhuntawa da gwamnati, saboda tun watan Yuni yake tsare. Sai dai ya nace cewa bangarorin biyu a shirye suke a sulhunta rikicin na shekara takwas cikin ruwan sanyi.

Abubakar ya yi da’awar cewa ya gudanar da ayyukan leken asiri tare da bayar da bayanan sirri ga ’yan ta’addan wadanda suka ba su damar samun nasarar hare-harensu ciki har da sace dalibai 276 na Makarantar Sakandaren ’Yan mata ta Gwamnati da ke Chibok da kuma kisan gilla ga daliban Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Buni Yadi.

Ya kuma yi da’awar cewa da shi aka kai hare-hare kan makarantun Maiduguri da Damaturu da Postikum da Mamudo. Ya ce: “Shekau ya bar maboyarsa da ke dajin Sambisa ya koma kan dutsen Mandara. Yawaita kai harin soji ya karya lagon mayakan Shekau da sauran kungiyoyin.”

Karanta:  'Yan Boko Haram 240 sun mika wuya bayan farmakin soji

Kuma ya ce, bangaren Albarnawi da Mamman Nur suna adawa da salon shugabancin Shekau.

Abubakar ya ce: “Lokacin fara kai hare-hare mun yi yaki kana bin da muka dauka aikin addini ne na kafa daular Musulunci inda mutane za su rayu cikin mutunci da martabawa. Amma bayan mamaye garuruwa da dama, sai Shekau ya fara nuna rashin imaninsa da rashin tausayin dan Adam. Kuma saboda yawan rashin imanin da kungiyar ta rika nunawa, wadansu daga cikin manyan kwamandojin ciki har da ni da Albarnawi da Mamman Nur, muka kalubalanci Shekau, muka bukaci a hanzarta kawo wannan tabargaza.” Ya kara da cewa: “Daga baya Albarnawi da Mamman Nur sun balle suka kafa nasu kungiyoyin. Shekau ne ke sa ake kai hare-haren kunar bakin wake da bama-bamai a kan fararen hula a Arewa maso Gabas. kungiyoyin Albarnawi da Mamman Nur ba su kai hari a makarantu da wuraren ibada da kasuwanni ko a kan yara da mata. Mun takaita yakinmu a kan hukumomin tsaro ne. kuma koda ma’aikatan nemo man ferur da aka sace kungiyar ba za ta kashe sub a.”

Ya ce: “Shekau ya yi kaurin suna wajen yin lalata da ’yan mata da sauran matan da aka sace da kuma sanya su yin harin kunar bakin wake. Yakan kashe mutane da sunan hukuncin yin karya ko sata ko tawaye. Shekau yana kashe mutane ba tare da wani dalili ba. Shekau ya bai wa kansa matsayin mai zargi kuma mai kara kuma alkali sannan mai zartar da hukunci wanda hakan ya yi hannun riga da koyarwar Musulunci. Kuma ana barin yunwa tana kashe yara da mata saboda mugun zalunci na Shekau.”

 

3640total visits,3visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.