Yajin Aiki: Gwamnatin Tarraya Zata Gana Da Assu A Yau Din Nan

Ministan Kodago, Dr. Chris Ngige zai gana yau din nan da Shugabannin Kungiyar Malaman Jami’a wato ASSU a kokarin shawo kan ‘Yan Kungiyar su janye yajin aikin da suka tsunduma ciki.

A wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Yada Labarai ya fitar yace wakilan gwamnati a wajen tattaunawar sun hada da Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu da abokin aikinsa Ministan Kudi, Kemi Adeosun.

Haka kuma ana tsammanin kasancewar Shugaban Ma’aikatar Albashi da Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa a gurin Taron.

Sanarwar ta waiwayi alkawarin da Kungiyar ASSUn tayi a zama na baya wanda aka gudanar ranar Alhamis 17 ga watan Agustan da muke ciki cewa zata gabatar da bukatun Gwamnatin Tarayya ga sauran ‘yan Kungiyar ta kuma dawo da ba’asi cikin mako guda.

Sanarwar ta ambato Ministan na kira ga ‘yan kungiyar Malaman Jami’an da su nuna halin dattako domin kuwa Gwamnatin Tarayya na duk wani kokari na dinke barakar da ta kunno kai tsakaninsu da ‘yan kungiyar ta ASSU.

Daily trust 29/08/2017

2397total visits,1visits today


Karanta:  A Jigawa wasu Dalibai 'sun kashe abokinsu don zargin luwadi'

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.