‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 15 a Kan Iyakar Najeriya

Wasu mahara da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun halaka mutane 15 suka kuma yi garkuwa da wasu mutane takwasa a wani kauye da ke kusa da iyakar Najeriya a yankin garin Kolofota na kasar Kamaru.

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan Boko Haram ne, sun harbe mutane 15 har lahira, kana suka yi garkuwa da wasu takwas a wani kauye da ke arewacin kasar Kamaru.Jami’ai sun ce ‘yan bidigar sun yi ta bude wuta ne akan kauyen Gakara da bindgogi masu sarrafa kansu, da tsakar daren Alhamis har zuwa wayewar garin Juma’a, sannan suka kona gidaje sama 30.

Shi dai kauyen na Gakara, yana wajen garin Kolofata ne, wanda ya sha fama da hare-haren ‘yan kungiyar ta Boko Haram, yana kuma da iyaka da Najeriya.

Jami’an cikin gida a kasar ta Kamaru, sun ce mutane da dama sun tsere daga kauyen inda suka nemi mafaka a sansanin ‘yan gudun hijirar da ke Kolofatan, wanda ke dauke da dubban mutane da suka tserewa rikicin Boko Haram.

A cikin ‘yan shekarun da suka gabata, kungiyar ta Boko Haram ta sha kai hare-hare a Kamaru da Jamhuriyar Nijar da Chadi, lamarin da ya kai ga kasashen suka kafa wata rundunar tsaro mai hadakar dakaru 8,700 domin tunkarar kungiyar.

Asalin Labari:

VOA Hausa

753total visits,3visits today


Karanta:  Rikici ya barke tsakanin al'ummar Hausawa a Lagos

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.