‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 11 a Najeriya

Tuni dai aka aike da tarin jami'an 'yan sanda don kubutar da mutanen da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a birnin Port Harcourt na jihar Rivers a kudancin Najeriya

Wasu ‘yan bindiga a Port Harcourt da ke kudancin Najeriya sun yi garkuwa da fasinjojin wata motar safa mutum 11 a yammacin Litinin din nan. Al’amuran garkuwa da mutane don karbar kudin Fansa a yankin na Port Harcourt ya yi kamari inda rahotanni ke nuni da cewa ko cikin watan nan ma anyi garkuwa da kimanin mutum 16.

A cewar wani daga cikin pasinjojin daya kubuta daga hannun ‘yan garkuwar Amiekro Princewill da misalin karfe 9 na daren jiya ne masu garkuwar suka tsayar da motarsu tare da bukatar su fito, suka kuma tisa keyarsu zuwa cikin daji amma mutum biyar suka kubce kafin zuwan jami’an tsaro .

Shima wani da ya kubucewa ‘yan bindigar Bright Belekwe ya ce ai bayan da suka gama shigewa da mutanen cikin daji ne jami’an tsaro suka iso wurin, kuma sun bincika amma basu kai ga gano inda suka boye ba.

Wannan dais hi ne karo na uku cikin wannan watan da ake garkuwa da mutane a birnin na Port Harcourt da ke jihar Rivers a kudancin Najeriya.

A wani taron manema labarai da kwamishinan ‘yansandan shiyyar Ahmad Zaki yak ira yau a shalkwatar yan sanda da ke Port Harcourt ya ce jami’an tsaro na ci gaba da aikin don ceto rayukan sauran fasinjojin.

 

 

Asalin Labari:

RFI Hausa

1049total visits,2visits today


Karanta:  Tasirin Sintirin Da Sojojin Najeriya Ke Yi a Sassan Kasar

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.