‘Yan Boko Haram 240 sun mika wuya bayan farmakin soji

Mayakan Boko Haram fiye da 240 ne suka mika wuya, bayan farmaki ta sama da kasa da dakarun hadin guiwa na kasa da kasa (MNJTF) suka kai a maboyarsu.

Wata sanarwa da rundunar ta MNJTF ta fitar, ta bayyana cewa yawancin mayakan sun fito ne daga yankin na tafkin Chadi.

Ta kara da cewa mayakan sun mika wuyan ne a sashe na biyu na sansanin soja a yankin Bagasola da ke kasar Chadi.

Dakarun na MNJTF da suka fito daga Najeriya, Chadi, Nijar da Kamaru sun fara aikin murkushe mayakan Boko Haram din da ke kasashen da aka yiwa lakabi da ”Operation Gama Aiki”.

An kuma tantance su tare da ajiye su a sansanin, inda Kwamandan rundunar Manjo Janar Lamidi Adeosun ya yi musu jawabi.

Kwamandan ya ce za a ba su horo a fannoni daban-daban na sana’oi, kamar yadda hukumomi da wasu kungiyoyi masu zaman kansu suka tsara.

Sojojin dai sun samu galabar toshe kafofin samun abinci da kayan fada zuwa ga mayakan, da hakan ya sa su da iyalansu kaura daga matsugunansu suka mika wuya.

Galibinsu dai sun mika makamansu a sansanonin soji mafi kusa da su a yankin.

Hakan dai ya kawo adadin mayakan na Boko Haram da suka mika wuyansu zuwa 460 kawo yanzu.

Bayanai sun nuna cewa akwai mayakan Boko Haram da dama a yankin na tafkin Chadi.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1104total visits,1visits today


Karanta:  Buhari ya yi alla-wadai da harin mujami’a a Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.