’Yan Boko Haram sun kashe mutum biyu a Adamawa

’Yan Kungiyar Boko Haram sun sake kai hari tare da kone kauyukan Muduvu da Nyibango da ke cikin Karamar Hukumar Madagali a jihar Adamawa.

’Yan Kungiyar Boko Haram sun sake kai hari tare da kone kauyukan Muduvu da Nyibango da ke cikin Karamar Hukumar Madagali a jihar Adamawa.
Harin ya auku ne bayan ’yan kwanaki da kai irinsa a kauyukan Ghumbili da Mildu inda mutane da dama suka bata.
Shugaban Karamar Hukumar Madagali, Malam Yusuf Muhammed ya fada wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya a ranar Talata a garin Yola cewa ’yan kungiyar Boko Haram din sun kai harin ne da misalin karfe 11 zuwa 12 na daren Liitinin din da ta gabata.
Muhammed ya bayyana cewa harin da aka kai shi ne na biyar a jerin hare-haren da ’yan kungiyar Boko Haram din suka kai cikin makonni biyu a yankin.
Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta kawo wa al’ummomin da lamarin ya shafa dauki.
Asalin Labari:

Aminiya

1410total visits,1visits today


Karanta:  An dauki tsauraran matakan tsaro a jihohin Adamawa da Taraba domin babar Sallah

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.