‘Yan Boko Haram sunzo makarantar mu sata ne, ba daukar mu ba – ‘Yan matan Chibok

Wani rahoto ya bayyana cewar ‘yan kungiyar Boko Haram basu je makarantar Chibok ba da niyyar daukar dalibai ‘yan mata akalla 276 da suka sace ba a shekaru biyu da suka wuce, illa dai kawai sun ziyarci wannan waje ne domin satar kayan gini.

Satar yaran dai kamar rahoton ya bayyana ya afku ne bayan sun rasa samun kayan da suke bukata inda suka yanke shawarar yin gaba da yaran. Wannan dai yana daya daga cikin bayanan wasu daga cikin ‘yan matan da suka sami ‘yancin kansu inda ake tsare da wasu yar zuwa yanzu.

Rahoton dai na yunkurin kungiyar Boko Haram da zuwa da summar satar kayan aiki wanda yaga baya suka buge da sace ‘yan matan Chibok a ranar 14 ga Aprilu na 2014 ya zo ne daga jaridar Vanguard wanda kuma jaridar Premium Times ta wallafa.

Haka zalika asalin rahoton da yazo daga Gidauniyar Thomson Reuters wanda labarin yazo daga wata ‘yar Chibok mai suna Adamu, ya bayyana cewar da farko takaddama ta afku sakamakon tattauna yadda a’ayi da ‘yan matan a yayin sace su.

Wadansu daga cikin shafukan na rahoton sun nuna cewar daga cikin ‘yan matan ne suka rubuta yadda lamarin ya kasance, ciki kuwa har da zaman su a dajin Sambisa a cikin harshen Turanci.

Ta bayyana cewar bayan daliba mai suna Adamu, an samu wadansu yara akalla guda biyu da suka bayar da gumunmanar rubutun rahoton a littafai da ‘yan kungiyar ta Boko Haram ta basu domin yin dasari.

1230total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.