‘Yan gudun hijra na karo-karo don ba ‘ya’yansu ilimi

Halin tagayyara da dugunzumar da rikicin ‘yan ta-da-kayar-baya na Boko Haram ya jefa wasu ‘yan gudun hijira, ba su sanyaya musu gwiwar ilmantar da ‘ya’yansu ba a sansanonin da suke samun mafaka.

‘Yan gudun hijirar sun tashi tsaye don nema wa ‘ya’yansu mafita ta hanyar kafa makarantar Islamiyya da taimakon kungiyar Women In Da’awa.

Wakiliyar BBC Badriyya Tijjani Kalarawi, ta ziyarci Tudun Mun Tsira, wani sansanin ‘yan gudun hijira da ba na gwamnati ba da ke unguwar Karmo a Abuja babban birnin Najeriya, inda ta ga yara na karatun islamiyya a wani waje da aka kewaye da langa-langa.

Malama Hassana Abdullahi, na daya daga cikin malaman da ke koyarwa a wannan islamiyya, ta kuma ce ita ma a sansanin take da zama.

Malamar ta ce da su uku ne ke koyarwa a makarantar amma sai iyayen yaran da ke zaune a sansanin suka lura cewa malaman sun yi kadan, don haka suka yanke shawarar karo wasu, idan ya so sai su rika karo-karo suna biyansu albashi a duk wata.

Hassana Abdullahi ta ce, wannan shawara da iyayen yaran suka yanke, ta yi matukar tasiri wajen samar da ilimi ga yaran da ke zaune a sansanin na Tudun Mun Tsira kasancewar ba ya karkashin kulawar gwamnati.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1488total visits,3visits today


Karanta:  Basarake ya kitsa shirin sace kansa a matsayin garkuwa

One Response to "‘Yan gudun hijra na karo-karo don ba ‘ya’yansu ilimi"

  1. Abdul Hamid ado buhari bkm   December 11, 2017 at 2:52 pm

    barkanku da aikace aikace inayi muku fatan alsheri allah yayi jagora

    Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.