‘Yan Kabilar Igbo Mazauna Adamawa Sunyi Allah Wadai Da Ayyukan Ta’addancin Kungiyar Masu Rajin Kafa Kasar Biafra Ta IPOB A Kudu Maso Gabashin Kasar

Lokacin da yake zantawa da Manema Labarai a Yola ranar Jumma’a bayan wani taro da mambobin Majalisar Tsaro ta Jihar, shugaban Cibiyar Al’adun Igbo a Jihar Adamawa Cif Obonna Paul Ibere ya zargi kungiyar ta IPOB da yunkurin kawo rikici a yankin kudu masu gabashi kasar.

“Duk wanda aka samu da aikata laifin da ya sabawa dokokin kasa kamata yayi a hukunta shi,” a cewarsa.

“Dubi wannan batu na IPOB a matsayin batun da aka kaddara ya faru, sai dai cewa wasu fusatattun mutane na kokarin kai lamarin ya wuce kima”

Ya ja hankalin sojojin da aka girke don samar da tsaro a gurin rikicin dasu kaucewa cin zarafin wadanda basu jiba basu gani ba.

Tun da fari Kwamishinan Yada Labaran Jihar ta Adamawa, Ahmad Sajoh cewa yayi an shirya taron ne don tabbatarwar ‘yan kabilar Igbo mazauna yankin kariya da zama lafiya a cikin jihar.

Ya  sake jaddada manufar gwamnatin jihar na tabbatar da kariya ga rayuka da dukiyoyin al’ummar dake zaune cikin jihar ba tare da nuna kabilanci ba.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

1945total visits,1visits today


Karanta:  An yi hatsaniya tsakanin magoya bayan Buhari da masu son ya sauka

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.