‘Yan Kannywood mafiya yawan mabiya a shafukan sada zumunta

Shafukan sada zumunta sun kasance kafofin sadarwa a tsakanin al’umma. Jaruman Kannywood suma ba’a barsu a baya ba inda mafiya yawan su ke rike da ragamar shafuka wadanda suka da dubunnan mabiya. Shafin Muryar Arewa ya samu leka wasu daga cikin wadannan shafuka domin zaluko Jarumai mafiya yawan mabiya wadanda suka yi fice a cikin masana’antar ta Kannywood.


Instagram

Shafin Instagram ya kasance dandali mafi shahara a tsakanin Jaruman masana’antar Kannywood inda mafi yawa kanyi amfani dashi wajen tura hotuna da suka shafi shirin fim dama rayuwar su baki daya.

1. Rahama Sadau: Shafin Jaruma Sadau ya kasance shahara a shafin na Instagram inda take da mabiya 957,134.

2. Hadiza Gabon: Jaruma Gabon ta kasance ta biyu a yawan mabiya a shafin Instagram da mutane 858,037.

3. Ali Nuhu: Sarki Ali na da yawan mabiya 813,684.

4. Fati Washa: Mabiya 739,785.

5. Maryam Booth: Mabiya 655,216.


Twitter

Yawa yawan Jaruman Kannywood basu cika ta’ammali da shafin Twitter ba. Duk da cewa Jaruman sun farga da wannan dandali a lokutan baya da Twitter ta fara tantance shafukan Jaruman irin su Ali Nuhu, Hadiza Aliyu, Rahama Sadau da dai sauran su.

1. Rahama Sadau: A bangaren shafin na Twitter shima Jaruma Sadau ta sake yin fintinkau inda ta kasancewa ta farko da yawan mabiya 168,296

2. Ali Nuhu: Sarki a wannan bangaren ya kasance na biyu inda ya jefo Jaruma Gabon daga mataki na biyu a shafin Instagram da mabiya 163,086

3. Hadiza Gabon: Gabon ta samu fadowa ta uku a wannan shafi na Twitter inda take da mabiya 134,093

4. Maryam Booth: 78,077

Karanta:  Dalilin da ya sa na fito a Barauniya - Hafsa Idris

5. Fati Washa: 75,866

Facebook

1. Ali Nuhu: Ali wanda aka fi sani da Sarki a masana’antar ta Kannywood ya kasance gwarzo mafi shahara a shafin Facebook inda yake da mabiya 1,636,580.

2. Rahama Sadau: Sadau a shafin Facebook ta kasance ta biyu inda Ali Nuhu ya kwado ta da kasa daga mataki farko a shafukan Instagram da Twitter inda take da 657,359.

3. Hadiza Aliyu: Jaruma Gabon ta sake maye gurbin na uku kwatankwacin shafin Twitter inda take da mabiya 415,305.

4. Aminu Saira: Saira duk da dai cewa shafin nasa ya gauraya da kamfanin sa na Hausa Empire shima ba’a barshi a baya ba inda yake da mabiya 84,457.

1404total visits,765visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.