‘Yan Kasashen Turai Sun Samu Sakon Su Fice Birtaniya

Kasar Birtaniya ta nemi gafarar wasu ‘yan kasashen Turai sama da 100 da suka samu sakon su fice daga kasar akan abin da ta kira kuskure. Matakin ya razana 'yan kasashen Turai da dama da suka samu sakon.

Ma’aikatar cikin gidan Birtaniya ta ce ta kaddamar da bincike kan yadda aka yi wasiku sama da 100 suka isa wajen ‘yan kasashen Turai da ke zama a kasar.

Mai Magana da yawun ma’aikatar cikin gidan ta bayyana cewar lallai an samu kuskure wajen aikawa da wasikun, kuma suna tuntubar duk wadanda suka samu wasikar domin kwantar musu da hankali.

Jami’ar ta ce suna sane da cewar babu sauyi kan dokar da ta bai wa ‘yan Yan kasashen Turai umurnin zama a Birtaniya.

Eva Johanna Holmberg, wata malaman jami’a yar asalin kasar Finland da ta ke auren dan Birtaniya ta ce ta kadu lokacin da ta samu wasikar.

‘Yancin Yan kasashen Turai na zama a Birtaniya na daga cikin batutuwa 3 da kungiyar Turai ke neman daddalewa da Birtaniya kafin tattauna yadda dangantaka za ta kasance a tsakaninsu nan gaba.

Asalin Labari:

RFI Hausa

607total visits,1visits today


Karanta:  Ina son dawowa amma sai likitocina sun sallame ni-Buhari

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.