‘Yan majalisar Nigeria sun sayi motocin ‘kece-raini’ 200

'Yan majalisar wakilan Najeriya sun saya wa kansu motoci na alfarma 200 kirar fijo 508 daga kamfanin kera fijo na kasar, Peugeot Automobile Nigeria Limited.

Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, Mr. Abdulrazak Namdas, ya shaida wa BBC cewa an sayi motocin ne domin ‘yan majalisar su samu damar gudanar da ayyukan kwamitoci da kyau.

Wannan lamari dai na zuwa ne a lokacin da ‘yan kasar da dama suke kokawa kan tsananin talauci da tsadar kayayyaki da ake fama da su.

“Duba da halin da kasar ke ciki ya sa mu ma ba mu sayi motocin duka a lokaci guda ba, don babu kudin da za a saye su a lokaci daya,

“Don haka sauran ‘yan majalisar sai daga baya za su samu, yanzu dai an fara bai wa sabbin zuwa majalisar ne wadanda ba su taba mallakar irin motocin ba,” in ji Honorabul Namdaz.

Mista Namdaz ya kara da cewa nan da karshen shekara za a kawo sauran motocin domin bai wa sauran ‘yan majalisar da ba su samu ba a yanzu.

Ya kuma ce majalsiar ta yanke shawarar sayen motocin kirar fijo ne saboda ganin cewa a Najeriya ake yin su, wanda hakan zai taimakawa kasar wajen habakar tattalin arzikinta.

A watan Janairun 2016 ne batun sayen sabbin motoci da majalisar za ta yi kan kudi dala biliyan 45 ya jawo ce-ce-ku-ce a kasar.

Sai dai ‘yan majalisar sun musanta wannan batu ina suka ce an zuzuta yawan kudin, har ma suka ce basussuka ne za a karbo a sayi motocin da su.

Sharhi, daga Halima Umar Saleh, BBC Abuja

Wadannan motoci dai ana sayensu daga aljihun gwamnati domin gudanar da ayyukan sa ido na kwamitoci, kuma ana fitar da kudin ne daga cikin kasafin manyan ayyuka na majalisar.

Karanta:  An yi hatsaniya tsakanin magoya bayan Buhari da masu son ya sauka

Bayan shekara hudu a lokacin da za a kafa sabuwar majalisa, ana iya sayar wa ‘yan majalisar da ke bukatar motocin inda za a cire daga cikin wasu kudade na sallamarsu. Ga wanda ba ya bukata kuma sai a karbi motar.

Kaza lika ‘yan majalisar da ba wannan ne karonsu na farko a majalisar ba kuma sun sha samun motocin, su ma ana sake ba su motocin.

Sannan kuma duk wata hidima ta motocin da za ta taso daga kan gyara zuwa shan mai duk majalisa ce za ta dinga daukar nauyin yi.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1032total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.