”Yan Nigeria na cikin wadanda aka fi bautarwa a Birtaniya’

Hukumomin tsaro a Birtaniya sun ce girman matsalar bauta ta zamanin da ake yi a kasar ta fi yadda ake tsammani a baya.

Hukumar kula da manyan laifuka ta kasar, NCA, ta ce, adadin da ake da shi a baya na mutanen da ake bautarwa ko tilastawa aiki dubu 13 kadan ne a cikin adadin da ake da shi, inda ake samun su a ko wanne manyan garuruwa da birni a Birtaniya.

Mafi yawan wadanda aka fi bautarwa ‘yan asalin kasashen Najeriya da Albania da Vietnam da Romania da kuma Poland ne, sai dai akwai ‘yan asalin Birtaniyan ma da abin ya shafa.

Yanzu haka ana gudanar da bincike 300, amma hukumar ta ce yayin da take duba batun, tana kara samun wasu sabbi.

Kungiyoyin kasashen waje ne ke harkar a bangarori daban-daban, da suka hada da gidajen abinci da kamun kifi da noma da gine-gine da wuraran wanke motoci da ma aiki a gidaje.

Wani darakta a hukumar NCA Will Kerr, ya ce, “A duk lokacin da muka sake yin bincike sai mun samu sabbin alkaluma.

Mr Kerr ya ce ya kadu matuka da abin da ya gani lokacin da aka kai farmakin kama mutanen, inda ko wanne babban aiki ke bankado wasu bincike daban.

Ya yi gargadi cewa fataucin mutane da ake yi don bautar da su ya yadu matuka a yanzu, ta yadda mutanen gari ma ke haduwa da wadanda ake bautarwar a kullum.

Daga hankali

Hukumar NCA ta ce ana samun karuwar bautar da mutane ne daga gungun masu fasa-kwauri na duniya saboda irin yawan kudin da hakan ke kawo musu, wanda ya fi a ce miyagun kwayoyi kawai suke sayarwa.

Ta yi gargadi cewar manyan hanyoyin da ake sa mutane aikin bauta sun hada da harkar sarrafa abinci da bangaren noma da gine-gine da ayyukan gida da wankin mota.

Karanta:  Za a Kai Gwamnatin Taraba kotun ICC

NCA ta ce alamun da ke nuna cewa ana bautar da mutum sun hada:

  • yanayin sanya tufafinsu
  • tabon ciwo da ake iya gani a jikinsu
  • alamun gajiya da gazawa
  • da salon da suke bi na zuwa aiki

Mene ne salon bauta ta zamani?

Wadanda suke fuskantar bauta ta zamani a Birtaniya sau da yawa a fili suke, suna aiki a wuraren yankan farce da gine-gine da mashaya da gonaki.

Masu fasa-kwaurin mutanen na amfani da intanet ne don jawo hankalin mutane da yi musu alkawuran karya na samun kyakkyawan aiki da ilimi ko kuma soyayya.

Wannan abu na iya shafar kowa daga maza har mata, yara da manya, amma ya fi yawa a tsakanin wadanda ba su da galihu sosai.

Mutane da yawa sun yi amanna cewa wadanda ke samu kansu cikin irin wadannan matsaloli suna kokarin kaucewa bakin talaucin da suke cikin, da rashin aikin yi a kasashensu da kuma yaki da ya addabe su.

Yin lalata da mutane na daga cikin salon bauta da aka fi sani ana yi wa mutane a Birtaniya, daga shi sai azabtarwa sai kuma tursasa mutane su aikata miyagun laifuka sai bautarwa da aikin gida.

Amma su iyayen gidansu da ke sa su a harkar suna samun makudan kudade.

Yadda ake bautar da ‘yar shekara 12

Mutane daga yankin Gabashin Turai da Vietnam da Najeriya sune wadanda aka fi kai wa Birtaniya don aikin bauta, in ji Mr Kerr said.

Ya bayar da misalin wata yarinya ‘yar shekara 12 daga Roma, wada aka tsayar da ita a kan iyaka aka kuma gano cewa ana bautar da ita ne.

Karanta:  Qatar: Wani Sanata zai hana Amurka sayar wa Saudiyya makamai

Ya ce, “An kawo ta Birtaniya ne don ta yi aiki da wani iyali, kuma mahaifinta ne ya sayar da ita, an kuma kawo ta wani gida don ta dinga kula da ‘ya’yansu tana kai su makaranta kullum tana kuma daukok su, ta kuma yi aikin goge-gogen gida.

“Shekararta 12, sa’ar karamin dana ce.”

Mr Kerr ya ce ba a kai ga gabatar da tuhuma aikata miyagun laifuka ba a kan masu cikin lamarin.

Ya kara da cewa wasu matsalolin da hukumomi ke fuskanta da ke kara damalmala batun shi ne yadda mutane ba sa fahimtar cewa bautar da su ma ake.

Asalin Labari:

BBC Hausa

476total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.