”Yan Nigeria Sun Ba Da Cin Hancin Naira Biliyan 400′

Jami'an gwamnati a Najeriya sun karbi cin hancin fiye da dala miliyan 110, wanda ya yi daidai da naira biliyan 400, in ji rahoton wani bincike da aka wallafa.

Rahoton ya bayyana cewa a kalla kusan ko wanne dan kasar da ya mallaki hankalinsa daya ne ya biya cin hanci a shekara.

Binciken wanda ofishin kididdiga na kasa NBS ya wallafa, ya nuna yadda cin hanci da rashawa ya yi wa ayyukan gwamnati katutu.

Rahoton ya kuma ce ‘yan Najeriya na kallon cin hanci da rashawa ne matsala ta uku a girma cikin matsalolin da Najeriya ke fuskanta.

Alkaluma sun nuna cewa a duk lokacin da dan Najeriya ya bayar da cin hanci yana kashe kimanin kashi 28.2 na albashinsa na wata ne.

Wannan na nufin cewa tun da masu bayar da cin hanci a Najeriya na biyan kimanin kashi 5.8 cikin 100 a shekara, sun kashe kashi 12.5 na albashinsu a matsayin cin hanci kenan.

A al’ada, ‘yan Najeriya basa son bayar da cin hanci, kamar yadda rahoton ya ce, kashi 85.3 na batutuwan cin hanci da rashawa na samuwa daga bangaren jami’an gwamnati kuma kashi 70 cikin 100 na lokacin a kan mika cin hancin ne kafin gudanar da aikin da suke bukata.

Hukumomin da wannan matsalar ta fi shafa a kasar su ne jami’an ‘yan sanda, sai kuma bangaren shari’a. Binciken ya bayyana cewa matasa ne suka fi samun kansu tsundum fiye da sauran ‘yan kasar.

Wannan shi ne karo na farko da wata gwamnatin Najeriya ke duba yawan cin hanci da rashawa a kasar.

Auwal Musa Rafsanjani, wanda shi ne wakilin kungiyar Transparency International masu fafutukar yaki da cin hanci da rashawa ya ce wadannan bayanan ba su bayar da mamaki ba.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1206total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.