‘Yan Okada Sun Fara Yajin Aiki A Jihar Legas

Masu sana'ar Okada a birnin Legas, wadanda yawancinsu daga jihohin arewa suka fito, sun shiga yajin aiki saboda a cewarsu 'yan sandan jihar na tursasa musu tare da tatsarsu kudade na ba gaira ba dalili.

Masu haya da babura da aka fi sani da ‘yan Okada a birnin Legas sun fara wani yajin aiki na sai “baba ta gani” sanadiyyar matakin da rundunar ‘yan sandan jihar ta dauka na fara kam asu muddin ba su bi wasu ka’idoji ba.

Rundunar ta bukace su, da su rika sanya wasu kaya da hula da kuma biyan wasu kudade. A cewar ‘yan kungiyar Okadan da akasarinsu ‘yan asalin jihohin arewa ne, jami’an ‘yan sandan na musguna musu tare da karbar kudade a duk lokacin da suka ga dama.

Wani dan Okada ya ce dokar sa riga da hula tare da yankar tikiti basu ki ba amma bayan sun sa hula da riga sun yanki tikiti, yan sanda zasu gansu su kuma kamasu. Ya ce idan mutum ya yi magana sai dan sanda ya soma duka. Wani lokacin ma da motarsa zai sa ya buge mutum kana ya ce ya kamaka shi.

Amma a cewar rundunar ‘yan sandan ta dauki matakan ne domin inganta harkokin tsaro a birnin na Legas. Duk da abun da ‘yan sandan suka ce, ‘yan Okadan basu gamsu ba saboda wai ana zaluntarsu.

Asalin Labari:

VOA Hausa

2066total visits,3visits today


Karanta:  Rundunar 'yan sandan jihar Osun ta damke wasu bata gari 26

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.