Yan Sanda a Jihar Ogun Sun Kama Masu Satar Yara

Rundunar yan sanda jihar Ogun a Najeriya ta tabbatar da kama wasu mata da na miji da suke satar kananan yara suna sayar dasu ga masu bukata.

Yan sanda na Ogun sun kama wadannan mata da na mijin ne dauke da wani yaro mai shekaru biyu da aka gano ba dansu bane. A makwanni biyu da suka wuce kuma yan sanda sun kama wani mutum da shi kuma yake cikin wannan sana’a ta satar yara.

Kakakin yan sanda jihar Ogun ASP Abimbola Oyeyemi yace mutane da suka kama, sun basu muhimman bayanai da zasu taimakawa yan sanda wurin gudanar da bincike da zai kai ga kama Karin mutane da dama da suke wannan mummunar sana’ar.

Kakakin na yan sandan jihar Yemi, ya gargadi iyaye da su kula da kai zirga zirgar ‘yayansu. Wani da aka sace masa ‘ya ya tattauna da wakilinmu a Ibadan, inda ya bayyana masa irin halin da yake ciki kwanaki uku bayan an sace masa diyarsa mai sheakaru hudu.

Asalin Labari:

VOA Hausa

916total visits,1visits today


Karanta:  'Muna sa ran dawowar Buhari nan ba da jimawa ba'

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.