‘Yan sanda sun cafke wasu Inyamurai barayin shanu

‘Yan sanda a jihar Ogun sun sami nasarar cafke wasu mutane 4 da ake zargi da satar shanu a yankin Ofada na Karamar hukumar Obafemi Owede na jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na jihar, Abimbola Oyeyemi, ya shaida cewar wadannan mutane 4, a farkon mako sun yi wa Muhammed Ruga da Babuga fashin shanu manya guda 2, a yayin da dubun su ta cika a kokarinsu na aikata wani fashin a yankin Orile Igbehin na Ofada.

“Wadanda ake zargi da aikata waccan aiki sun hada da, Manu Abuchi, Onyeka Okafor, Francis Onyeka da Hafiz Mustapha wadanda suka farwa makiyayan guda 2 da adduna, suka kuma daure su bayan sun yi musu mugun duka, da kuma awon gaba da shanu guda 2” inji Kakakin rundunar ‘yan sandan.

 

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Nigerian

2366total visits,1visits today


Karanta:  Ba Wanda Zai Cire Magu - Osinbanjo

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.