‘Yan Sanda Sun Kama Mutum 3 Da Kawuna Da Hannayen Mutane A Osun

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Osun ranar Talata tace ta kama wasu maza su uku da kawunan mutane biyu da hannaye a jihar.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Mr Fimihan Adeoye ne ya fadawa manema labarai cewa an kama wadanda ake zargin ranar 29 ga watan Agusta a wajen binciken ababan hawa

“Ranar 29 ga watan Agusta da misalin karfe 1:02 na yamma ‘yan sandan sintiri suka tsayar da wani babur dauke da mutane biyu a kai a Agboro kan titin  Ogbomosho hanyar zuwa Oyo.

“Duba mutunen da ke kan babur din keda wuya sai aka same su dauke da hannaye da kan mutum a cikin jaka, nan take aka kama su,” a cewarsa.

Adeoye ya kara da cewa, a wani lamarin irin wannan kuma, a dai wannan rana da misalin karfe 11:30 a daidai farfajiyar Oba a Moro Ipetumodu aka kama wani mutum maisuna Adeniyi Adeyeye da kashin kan mutum

A cewarsa ‘yan sanda na musamman dake aiki a Hedikwatar ‘Yan Sanda ta Ipetumodu suka kama wanda ake zargin inda suka mayar da shi Sashin Bincikar Manyan Laifuffuka na Jihar.

A ta bakinsa kokon kan da aka samu gurin wanda ake zargin ana zargin an ciro shi ne daga kabari duk da yake dai har yanzu ana gudanar da bincike kan lamarin.

Adeoye ya kara da cewa da zarar an gama bincike za a kai wadanda ake zargin kotu.

Daily trust 6/9/2017

692total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.