‘Yan Sanda Sun Zargi Kwankwasiyya Da Laifi Bisa Rikicin Da Ya Faru Ranar Hawan Daushe

Hukumomin ‘Yan Sanda a Kano sun dora laifi kan magoya bayan Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bisa zargin haifar da rikicin siyasar da ya bar mutane da dama cikin rauni satin da ya wuce a Kano.

Za a dai iya tunawa cewa mutane da dama magoya bayan Kwankwasiyya ne suka jikkata sakamakon fadan da aka gwabza tsakanin magoya bayan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje lokacin Hawan Daushen da aka gudanar a Kofar Kudu, fadar mai martaba Sarki dake Kano.

Lokacin da yake ganawa da manema labarai a madadin Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Rabi’u Yusuf, Kakakin ‘Yan Sandan Jihar DSP Magaji Musa Majia cewa yayi tsagin APC kuma mambobin darikar Kwankwasiyyar ne keda alhakin fadan.

Inda yace dubun dubatar mutanen sun taro a Asibitin Hasiya Bayero da magoya bayansu wadanda suka zo daga Sokoto, Kogi da sauran makwabtan jihohi dama kananan hukumomin jihar da nufin tarwatsa taron hawan daushen da masarautar kano ke shiryawa.

Majiyan dake maida martani lokacin wani taron manema labaran da ‘Yan Kwankwasiyyar suka shirya cewa yayi “Duk da cewa taron ba na siyasa bane, amma sai ‘yan Kwankwasiyyar suka rika cewa “Ba mayi” Ba mayi” “Ba mayi”. Sun ringa fadar hakan ne lokacin da tsagin Kwankwasiyar suka hango tawagar Gwamnan Jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje na kusatowa gurin taron inda suka fara tarwtsa tawagar.”

Majia yayi bayanin cewa da gangan suka haifar da yamutsi, nan take fada ya barke tsakanin darikun na APC biyu, amma shiga tsakanin da ‘yan sanda sukayi cikin gaggawa ya dawo da doka da oda.

Ya kuma ce “An sami damar tsairatar da wasu fitattu daga cikin ‘yan Kwankwasiyyar wadanda suka hada da tsohon Kwamishinan Jihar, Dr Yunusa Adamu Dangwani, tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar, Dr Rabi’u Suleiman Bichi, tsohon Darakta kan Harkoki na Musamman, Alhaji Dan Yaro Yakasai, inda ‘yan sanda suka raka kowanne gidansa lafiya.”

Karanta:  INEC ta dage kiranyen Melaye

Ya kuma bayyana damuwarsa cewa abin bakin ciki ne ace wadanda suka jawo faruwar lamarin sun juya laifin kan jami’an ‘yan sandan da suka tseratar da rayuwarsu.

Ya kuma tabbatar da cewa babu wata farfaganda, ko wani matsi, ko kin fadar gaskiyar da zasu sa ‘yan sanda kin yin aikinsu na samar da doka da oda

“Rundunar ‘Yan Sanda na gargadin duk wani mai son haifar da yamutsi ta kowacce hanya cewa bazasu saki jiki suna kallon ‘yan daba na cin karensu ba babbaka ba a jihar, a cewar ta Kakakin na ‘yan sanda

Daily trust 8/9/2017

1516total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.