‘Yan sandan Kano suka cafke masu sace mutane a dajin Falgore.

Rundunan yan sandan jihar Taraba dake arewa maso gabashin Najeriya ta tabbatar da kissan wasu matasa da suka addabi jama’a wajen garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Anyi nasarar kame wasu mutane masu garkuwa da mutane tare da hallaka su a cikin jihar Taraba, Mutanen da aka kashe an same su da bindigogi da wasu mugayan makamai kuma kafin mutuwar su sun bada tabbacin cewa ba shakka suna aikata wannan danyen aikin.

Rundunan yan sandan jihar Taraba dake arewa maso gabashin Najeriya ta tabbatar da kissan wasu matasa da suka addabi jama’a wajen garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Kamar yadda bayanai suka tabbatar Matasa da suka harzuka ne suka kashe wasu samari guda hudu da ake zargi masu satan mutane ne su yi garkuwa da su, kuma lamarin ya faru a kauyen Tella a karamar hukumar Gassol na jihar Taraba.

Bayanai sun nuna cewa wadanda aka kashen sun dade suna addabar mazauna garin na Tella da fashi da kuma garkuwa da mutane kafin su fada ragar yan sakai na yan banga.

Hakan kuma rahotanni sun bayyana cewa an samu bindiga da wasu makamai a hannun wadanda aka kashen, kuma sun shaida wa wadanda suka kama su cewa iyayen gidansu na cikin daji wadansu kuma na cikin garin Jalingo.

Kakakin rundunan yan sandan jihar Taraban David Misal ya tabbatar da aukuwan lamarin tare da gargadin jama’a da su daina daukan doka a hannu.

Daga shekarar da ta wuce zuwa bana an sace sama da mutum 64 a kananan hukumomin Gassol da Bali, inda bayanai suka ce an biya sama da Naira miliyan 100 kudin fansa kafin sako su.

Asalin Labari:

Muryar Amurka

680total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.