‘Yan Sandan Saudiyya sun lakadawa mahajjatan jihar Nasarawa duka

‘Yan sanda a kasar Saudiyya sun lakadawa wasu Mahajjata daga Jihar Nassarawa duka, har daya daga ciki ya ji rauni a kansa.

Bincike ya nuna cewar, Mahajjatan wadanda suka sauka a kasa mai tsarki ranar laraba an garkame su a filin jirgi na Madina kusan tsawon awanni 9 kafin faruwar al’amarin.

Wani ma’aikaci na Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Nasarawa, Mallam Lawal Ahmad ya shaidawa wakilin jaridar Daily Trust cewar sai bayan da aka gama bincikar wadannan mahajjata a wurin tace fasinjoji kuma ba a samu komai na laifi  a tare da su ba, wannan lamari ya faru.

“Ma’aikatan shige da face sun kammala duba su suka ce su wuce, sai kuma wadannan ‘yan sanda suka dakatar da su sama da awa 9, daga baya kuma suka umarce su da su shiga wani daki” inji Malam Lawal.

“A nan ne fa saboda rashin sanin niyyarsu, suka tunkuda su cikin dakin suka kama da duka har aka ji wa daya rauni a kansa, wanda daga baya aka masa magani suka sallame su”.

Jami’in Hukumar kula da aikin hajji ta kasa dake birnin Madinah, Dr. Bello Tambuwal ya tabbatar da lamarin tare da shade cewar tuni Hukumar ta aika da korafi ga hukumomin da abin ya shafa domin bincike da daukar mataki. Tambuwal ya kara da cewar, ba za su zuba idanu ba a rinka cin zarafi da mutuncin mahajjata ba.

 

 

Asalin Labari:

dailyTrust, Muryar Arewa

1759total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.