‘Yan Sandan Spain Sun Kashe Maharin Barcelona

Jami’an ‘Yan sandan Spain sun halaka Younes Abouyaaqoub da ake zargi da kai harin Bercelona da ya kashe mutane 16 tare da jikkata sama da 100, akasarinsu ‘yan kasashen ketare.

Jami’an ‘Yan sandan sun harbe Abouyaaqoub mai shekaru 22 har lahira a yankin Sabirat mai nisan kilomita 60 daga Bercelona, lokacin da ya ke kokarin ficewa daga birnin.

A safiyar yau ne dai gwamnatin Spaniya ta sanar da kammala gano dukkanin mutane 16 da harin na Bercelona ya ritsa da su, ciki har da ‘yan kasar 6 da kuma ‘yan kasashen waje 10.

A cewar Ministan Harkokin Wajen kasar, daga cikin wadanda harin ya shafa har da ‘Yan Italiya uku da ‘Yan Portugal 2 da dan Belgium guda da kuma dan Canada.

Sauran sun hada da wani Ba’amurke daya da kuma wani dan Birtaniya mai ruwa biyu. Kananan yara guda biyu na cikin wadanda suka mutu a harin.

A cewar wata sanarwa da Ministan Shari’ar kasar Carles Mundo ya fitar ga manema labarai, tuni aka sanar da iyalan wadanda harin ya ritsa da su.

Cikin mutane 120 da suka jikkata, akwai Faransawa da Jamusawa da ‘Yan Birtaniya da ma ‘yan Netherland.

Asalin Labari:

RFI Hausa

862total visits,1visits today


Karanta:  Alhazan duniya sun fara aikin Hajji a yau

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.